GWAMNATIN KATSINA TAYI WA BUHARI ZAGON KASA A ZABE

0

GWAMNATIN KATSINA TAYI WA BUHARI ZAGON KASA A ZABE

Inji Kabir Murja


Daga taskar labarai
Shugaban APC akida bangaren Abu sama ila isa funtua Alhaji kabir murja yace gwamnatin katsina ta APC tayi wa shugaban kasa Buhari zagon kasa a zaben da ya gabata.
Kabir murja na wannan jawabin ne a wani taron manema labarai da ya Kira da yammacin yau Talata
Kabir murja yace sunayen da wata jarida ta fitar gaskiya ne,illa kawai gwamnatin taga wutar gasa Kanta ce ta janye ta kuma karyata
Murja yace a wannan gwamnatin suna da labarin yadda aka taimaki Atiku ta karkashin kasa a katsina don yayi nasara a zaben da ya gabata.
Murja yace mafi yawancin wadanda ke cikin gwamnatin katsina ba masu kaunar Buhari bane saboda har gwamnan yace da kudin gwamnatin tarayya ake yakarsa bayan gwamnan yasan cewa Buhari yaki yake da cin hanci da rashawa.me wannan ke nufi inji kabir murja .
Jaridun taskar labarai da the links news zasu saki cikakken bidiyon taron manema labarai da kabir murja ya gabatar .yau zuwa gobe.
………………………………………………………………………..
Taskar labarai da the links news jaridu masu rijista dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta na social media layin Kira ko whazzap 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here