GIDAUNIYA BADAMASI BURJI TA CANCANCI YABO

0
660

GIDAUNIYA BADAMASI BURJI TA CANCANCI YABO
Daga zaharadden Ibrahim kallah
Taimakon marasa galihu da bada tallafi ta kowacce fuska ba kowanne dan adam ne Allah ya ba wa zuciyar hakan ba. Allah ya wadata wasu mutane da dinbin arziki, wanda Hausawa kan kwatanta dukiyarsu da fam taba sama, amma fitar da wani kaso daga cikin wannan dukiya don tallafa jama’a ta fuskar lafiya ko ilimi da wasu bukatu na yau da kullum sai ya zamo jidali, domin suna ji kamar za su yanki naman jikinsu ne.

Abin ba haka yake ba a gurin Badamasi Shu’aibu Burji, wanda ya kasance marubuci, dan jarida kuma dan kasuwa. A ranar Litinin ne 14 ga Watan Oktoba, 2019 mutane daga sassa daban-daban na kasar nan suka yi dafifi a garin Burji da yake karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano, don halarta bikin kaddamar da bada tallafin sana’oi ga ‘yan mata tare da tallafin karatu ga ‘yan makarantun sakandire.

An gudanar da wannan al’amari ne karkashin Gidauniyar Badamasi Burji wadda ta yi nasarar samar da makaranta ta zamani mai ginin bulo da bula, dake dauke da azuzuwa ashirin wanda tuni an kammala guda goma, sannan an yi wani babban gini a cikin harabar makarantar. Duk da cewa wasu azuzuwan ba su kammala ba, amma yara sama da dubu uku da dari shidda ke karatu a wannan makarantar kyauta, tare da basu unifom da litattattafai kyauta.

An bude taron ne da addu’a daga bakin Alhaji Isa Jaa, wanda ake yi wa lakabi da dattijon arziki. Wannan taro ya samu jarogranci Alh. Ahmad Rabiu, wanda yana tsaka da wannan aikin arziki ne, labari ya iso na tabbatar da sunansa a jerin kwamishinoni da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, OFR ya sake ba wa dama su kasance a tare da shi. Alh. Ahmad Rabiu a baya shi ne kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu tare da Harkokin Yawon Bude Ido na jihar Kano. Shugaban taron ya yabawa Badamasi S. Burji bisa wannan aikin alheri, ya kuma bukaci a yi koyi da shi. A cewarsa irin wadannan ayyuka nagari da jin kai ke sa wa wadanda ba musulmi ba su kaunaci addinin musulunci. A saboda haka ya yi kira da a cigaba da jawo mazauna wajen da aka fi sani da maguzawa a jiki, hakan zai sa su kaunaci addinin musulunci. Haka abin yake, domin hadisi ne guda da yake nuna zuciyar dan adam a gina ta ne abisa son wanda yake kyautata mana.

A jawabin mai gayyar, Badamasi S. Burji ya bayyana cewa ya fito ne daga babban gida wanda ke dauke da iyali sama da dari biyar, amma sai ya kasance su uku ne kacal suka samu damar zuwa makarantar Sakandire. Wannan yasa ya dauri niyyar sauya tunanin mutanensu akan ilimin zamani, domin ya ga amfanin ilimi a rayuwa. Alh. Badamasi Burji ya yi waiwaye baya inda ya tuno lokacin da yake tallar waina da alkaki a kauyen nasu, wanda wannan al’amari ya taba zuciyar dattijan da suke gurin, musamman wadanda sun sha sayen waina a gurinsa a wancan lokaci. Wannan tarihi ba ya bukatar kara kafa hujja don mutanen garin su gasgata amfanin abin da aka kawo musu, ai sun gani a zahiri. Burji ya tabbatar da cewa an samu cigaba sosai a yankin na su, inda ya bada misali da yara 120 da suka rubuta jarrabawar shiga sakandire, sannan guda 109 suka samu nasara. Wannan shi ne babban dalili da ya sa ya ga dacewar bada tallafin karatu ga wadannan yara tare da ‘yan mata da aka koyar sana’oi. An gabatar da basa tallafi ga yara maza da mata, wanda daga cikin akwai yarinya mai lalurar kafa, amma haka bai taba kwazonta ba.

Tun a farko, ya yin jawabin maraba daga Hajiya Nana Asama’u Gwadabe ta yaba da yadda mutanen Burji suka karbi wannan yunkuri. A cewarta baya ga ‘yan mata da suke cin gajiyar wannan gidauniya, iyaye mata da maza suna bukatar su ma su dandani romon wannan abin arziki da ake gudanarwa. Ta kara da cewa wannnan gidauniya na bada gudunmawa ga ilimin manya, sannan tana koyar da mata sana’oi da suka hada koyon yin man shafawa da turare da sabulu da man wanke gashi da sauransu.

A jawabin uwar taron, Farfesa Gaji Dantata ta bayyana cewa ta san Badamasi a matsayin mai kyauta da jin kai, amma ba ta taba zaton ya kai haka a kishin al’ummarsa ba, sai da ta zo Burji. Ta bayyana cewa ya samu cigaban rayuwa da ke sa mutum ya manta mafarinsa, amma ya ki amintuwa da rudun alatun rayuwar, ya dawo mafarin nasa ya assasa samar da ilimin yara. Farfesa Gaji wacce take kwararriya a bangaren bayar da ilimi na masu bukata ta musamman ta nuna mihimmancin dake cikin bayar da ilimi ga mata da yara, wanda rashinsa kan jefa kwakwalen yara yin munanan tunane-tunanne, wanda a karshe zai kai su ga aikata wasu munanan ayyuka.

Hakika abin da Farfesa ta fada haka yake, Badamasi zai iya yin duk wani abu da ba ka zato. Mun yi mu’amula mai tsawo a matsayinmu na marubuta, sannan na yi masa sakatare a lokacin da yake rike da shugabancin Kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA), reshen jihar Kano. Har gobe muna kira shi da jirgin Annabi Nuhu, domin idan abubuwa suka hargitse a kungiya aka rasa yadda za a fita, ko kuma aiwatar da wani babban aiki, to Badamasi ne mafita. Na tabbata ba marubuta ba ne kadai suka shaida hakan a cikin kungiyoyi yake ciki. Na kan kwatanta zuciyar Badamasi da ta marigayi Muhammadu Adamu Dankabo, wanda aka yi imani kyauta da karimci da taimako na gudana a cikin jininsa.

Sakataren Ilimi na karamar hukumar Doguwa shi ma ya albarkaci wannan taro inda ya bayyana jin dadinsa ga yadda ilimi yake samun tagomashi a yankin. Ya bayyana cewa sanda ya hau kujerar sakataren ilimi ya yi kokarin samun al’kaluma na dalibai da suke yanki. Ga mamakinsa, alkaluma dalibai na yanki Burji da aka kawo masa ya fi na ko’oina a yanki, hakan yasa ya yi shakkar shahihanci wadannan alkaluma. Wannan yasa ya yi tattaki da kansa har Burji, wanda abin da ya gani ya wuce yadda yake tsammani. Sakataren ya amince wannan gagarumar nasara da aka samu ko shakka babu tana da nasaba da irin ayyukan bada ilimi da gidauniyar Badamasi Burji ke aiwatarwa. Ya yi godiya ga shugaban gidauniyar da fatan zai cigaba da wannan aikin lada da ya dorawa kansa.

Yayin gudanar da taron, na samu zantawa da Alh. Aminu Bayero Indabawa wanda yake matsayin uba ga Badamasi, kasancewar abokin babban dansa da ya rasu. Alh. Aminu ya shaida da mun cewa dawainiyar da Badamasi yake da shi da yadda ya dauke shi a matsayin uba, ko dan da ya haifa iya abin da zai iya yi masa kenan. A cewarsa mutum ne da ya san yakamata, tare da jin kan alumma wanda hakan ya zamar masa tsani da mabudi a cigaban rayuwa.

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron akwai wakilin shugaban karamar hukumar Doguwa da Hakimin Doguwa da Dagacinsa ya wakilta, da sauran dagatan dake yanki. Hakan nan akwai manyan aminai da abokan aiki na Badamasi S. Burji irinsu Alh. Saidu Fanyabo, marubuta da ‘yan jaridu na tarayya da jiha, a inda Muhammad Aminu Jolly ya kasance babban mai gabatarwa a yayin taron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here