YADDA DAHIRU MANGAL YA KUSA HAUKATA MAI SHAYI

0

YADDA DAHIRU MANGAL YA KUSA HAUKATA MAI SHAYI

Daga Taskar Labarai

Akwai wani mai shayi wata rana yayi mani korafin jarinsa yayi kasa, na dau alwashi a zuciya ta da wasu kudi sun fado mani zan agaza masa.

Allah cikin ikonsa wani kudi suka zo mani na ware na mai shayi kamar yadda nayi niyya, naje na duba teburin mai shayi don in bashi abin da nayi niyya, amma baya nan. Kwana uku ina duba teburin mai shayi bayanan, sai na damu.

A cikin kwana na hudu sai na nufi teburin na yi masa kallo a tsanake irin nazarin da masu bincike kan yi ma wurin da ake zargin an aikata laifi ko aka aikata laifin ( Crime Scene)
Bayan wannan nazarin a tsarin bincike sai kuma wa zakayi wa tambaya?

Nayi balaguro da idanu na sai na hangi wani maigadi ya kura mani ido kamar kamar kwarton da ake zargi. Sai na nufi wajensa na ce don Allah ina neman mai shayin nan ne.

Maigadin nan yace, “ai mai shayi tun da ranar nan ya shiga nan wajen aiki ya gaida Alhaji Dahiru Mangal ya fito yana dariya a ranar ya yi shayi amma tun daga ranar bai kara fitowa ba”.

Nace Meeee? Mai gadin yayi wata bazawarar dariya yace, “abin da nasan ya faru kenan”.

Aka kara kwanaki biyu mai shayi ban ga ya fito ba, sai na nemi inda gidansa yake na je kafin ina isa gidan sai nayi abin da masu bincike ke kira hawainiya da harshenta kafin a ganka.

Ina a wani wuri sake ina kallon gidan da yanayin shiga da fitar masu karakaina a gidan, naga ba wata alamar damuwa ko bakin ciki, sai na tunkari gidan kai tsaye wani yaro dan makimanci ya fito zai je wajen aike, sai nace masa kai ina mai shayi sai yace, “Baba?” Nace eh, yace “ayya ai yayi tafiya”.

Nace yaushe yace, “tun kwanaki” nace ina ya tafi yace, “ban sani ba na tashi da safe aka ce mani yayi tafiya, amma daren da zai yi tafiyar naji yana magana da mama yana fadin sunan Dahiru Mangal”.

Nace to, na bashi kati mai dauke da sunana da lambobin waya nace kai ma mamarka kace in ya dawo mai wannan katin yana neman sa, haka ake yi don duk abinda ya taso a nemo ka.

Na dawo gida lamarin na mani yawo a zuci da kwalwa, kwana biyu bayan zuwan gidan mai shayi ina gida da safe ina jiran matata ta ga mani dumame watau zazafen tuwon da aka ci da dare.

Sai aka ce ana sallama ina fita sai ga mai shayi nace a Malam lafiya ka tafi ba sanarwa ko ban kwana?

Yace, “ai tafiya nay”, nace kamar ya? Ya yi wata budurwar dariya ya buga kafa ya juya yace, “wata safiya ina a nan sai aka ce mani ga Dahiru Mangalya shiga can duba aiki, nace bari inje in gaida shi na shiga bayan mun gaisa sai yace mai shayi ya sana’a nace Alhamdulillah sai kawai ya saka hannu aljifu ya dumtso ya miko mani. Alhaji duk yan dubu dubu ne, na kasa kirgawa na kagara ruwan shayin ya kare in tafi gida.
A gida na kulle daki, wohohoho Alhaji naga kudi na fitar da karin jari a waje guda na biya matata bashi na yi wa mata kyauta na fitar da karo abincin cikin gida na ajiye wasu. Dama na Dade banje gida dubiya ba shi ne na tafi. Sai jiya na dawo.”

Mai shayi ya yi dariya ya buga kafa yace, *”DANA GA KUDIN KUSAN HAUKACEWA NAYI DON DADI”*. Ya kara da cewa, “don Allah duk in kaga Mangal ka fada masa ina godiya. Allah kara arziki da nisan kwana muka taba hannu da jijjigawa ya yi bankwana ya tafi.

Danjuma Katsina ya rubuta, rubutun nan don Jaridar Taskar Labarai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here