DALIBAN NIJERIYA MASU KARATU A KASASHEN WAJE NA KARA FITO DA MARTABAR NIJERIYA A IDON DUNIYA .

0

DALIBAN NIJERIYA MASU KARATU A KASASHEN WAJE NA KARA FITO DA MARTABAR NIJERIYA A IDON DUNIYA .

17 ga Oktoba, 2019.

Makarantar Ma’ahad Muhammad N Sadees Li Takweenil A’Imma da ke Rabat, babban birnin kasar Morocco ta zabi wani matashin dalibi daga jihar Katsina wanda ke karatu a kasar domin jagorantar sallar Juma’a a babban masallacin makarantar a wannan mako. Dalibin mai suna Sayyid Munir Adamu Koza ya samu nasarar jarabawar da ake yi wa daliban makarantar kafin su samu damar jagorantar sallar Juma’ar. Makarantar Ma’ahad tana da dalibai daga kasashe daban-daban na duniya kamar, Faransa da Côte D’Ivoire da Gambiya da Sinigal da Guinea da Gabon da Mali da Maroko da Nijeriya da sauran su. Bayan shi, hukumar makarantar ta sake zabar wasu daliban guda uku, Mallam Miftahu Ibrahim Shira daga jihar Bauchi da kuma Mallam Idrees Gyalgyal daga jihar Sakkwato wadanda za su jagoranci salloli biyar a masallacin makarantar na tsawon mako guda. Babban Limamin Masallacin kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Ahmad Maqary ya bayyana wannan mataki da daliban Nijeriya masu karatu a Maroko suka taka da abun yabawa matuka, inda ya yi addu’a da fatar alheri gare su da sauran daliban Nijeriya wadanda ke karatu a kasashen duniya daban-daban.

Daliban Nijeriya da ke karatu a kasashen duniya sun dade suna taka muhimmiyar rawar a-zo-a-gani a makarantun da suka je karatu, ko a ‘yan watannin da suka gabata wani dalibi mai suna Ustaz Garzali Tanimu ya zama gwarzon dalibi a wata makaranta da ke kasar Saudiyya, haka ma wani dalibin a watan Maris din shekarar 2018, Malam Bashir Dodo mai karatun digirin digirgir a Brunei da ke Landan ya lashe kyautar dalibin da ya fi nuna hazaka kan dabarar gano illar ciwon ido.

A zantawar da muka yi da ‘Sabon Limamin Ma’ahad’, Sayyid Munir ya ce Allah ne ya zabe shi a wannan matsayi, ba domin kasancewar ya fi kowa ba, inda ya yi wa Allah godiya a bisa hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here