0

An Kafa Cibiya Don Tunawa Da Dakta Yusufu Bala Usman

A kokarinsu na tabbatar da cewa, gudumwar da marigayyi Dakta Yusufu Bala Usman ya bayar a fannin bunkasa rayuwar al’umma da kuma bunkasar ilimi a kasar nan basu bace ba, makusanta da abokan aikinsa sun kafa wata cibiya ta musamman don tunawa da shi, wannna bayanin ya fito ne a wata takardar sanarwa da shugaban cibiyar Dakta Olusegun Osoba ya sanya wa hanun aka kuma raba wa manema labarai a garin Zariya.
Bayaninn ya kuma na cewa, cibiyar da za ta kasance a garin zariya ta jihar Kaduna, za ta bayar da dama ga manya da kananan masana da ‘yan boko su gudana da bincike da yin nazari a kan abubuwan da suka shafi kasarmu Nijeriya musamman binciko hanyoyin da za a kara samun hadin kanta da bunkasar tattalin arzikinta gaba daya. “Wadannan suna daga cikin manya manyan akidun marigayyi Dakta Yusufu Bala Usman, wanda aka Haifa a sherkatar 1945 Allah ya kuma yi masa rasuwa a shekarar 2005, cikin abubuwan da ya gabatar a wancan lokacin, kusan fiye da shekara 40 da suka wuce, har yanzu in aka yi aiki dasu za su yi maganin matsaloin da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu’’ inji sanarwar.
Haka kuma sanarwa ta bayyana cewa, kafa cibiyar ya zama dole ne don akwai yakinin cewa, in har aka yi amfani da matakai da bayanan da Dakta Yusuuf Bala Usman ya fitar don magance matsalolin Nijeriya da tuni mun yi nisa da ficewa daga dimbin matsalolin da kasar nan ke fuskanta a ‘yan shekarun nan.
An kafa cibiyar ne don taskacewa tare da samar da yanayin da zai haifar da tataunawa don ciyar da Nijeriya da Afrika gaba, hakan kuma ana saran zai ceto dimbin ‘yan Nijeriya daga kangin bauta da talauci da kuma babakere irin na ‘yan mulkin mallaka tare da samar da cikkaken kasa mai ‘yanci da al’umma za su amfana da mulkin dimokradiyya yadda yakamata. Cibiyar wadda za ta samu babban hedikwata a unguwar GRA dake Zariya a jihar Kaduna.
Ciki aikin farko farko da cibiyar za ta fara fuskanta sun hada da sake wallafa fitattatun littatafan da marigayyi Dakta Yususfu Bala Usman ya rubuta a zamanin rayuwarsa wadanda suka hada da ‘For the Liberation of Nigeria da Nigeria Against the INLF, da ‘The Manipulation of Religion in Nigeria, 1977-1987’ ana sa ran fitar da wadannna litattafan a ‘yan watanni masu zuwa.
Wannan gaggaurumin aikin za su samu kulawar kwararrun masana wadanda suka yi fice a fannoni daban diban na rayuwar bil adam, cibiyar zai samu Dakta Olusegun Osoba a matsayin shugaba yayin da Norma Perchonock za ta taimaka masa, haka kuma akwai Farfesa Gideon S. Tseja da dan marigayyin kuma magajinsa, Attahiru Bala Usman da Farfesa Osman A. Tar sai kuma Hajiya Hadiza Bala Usman.
Wakilinmu ya binciki tare da tattaro takaitattcen tarihin wadanda za su shugabanci wannan cibiyar, ga kuma abin da ya nakalto muku.
Dakta Olusegun Osoba
Dakta Segun Osoba aboki ne na kusa ga marigayyi Dakta Bala Usman na tsawon shekaru tare suka rubuta shaharraren rahoton nan na daftarin tsarin mulkin Nijeriya na shekafar 1976, wanda aka wallafa a shekarar 2019, ya kuma samu karbuwa kwarai a gaske a sassasan kasar nan. Ya yi aikin karantarwa a sashin tarihin na jami’ar O.A.U., Ile-Ife ta jihar Osun a tsakanin shekarar 1967 zuwa 1991. A halin yanzu ya yi ritaya, yana kuma zaune ne a garinsu dake Ijebu-Ode.

Norma Perchonock
Norma Perchonock abokiyar aiki ne na kut da kut ga Dakta Bala Usman tun daga shekarar 1970. Ta yi karatunta ne a jami’ar Temple dana Northwestern Unibersities dake kasa Amurka. Tana kuma cikin malamai na farko da suka kafa sashin karantar da zamantakewar al’umma ‘Sociology’ na jami’ar ABU Zariya, ta kuma cigaba da karantarwa tun daga shekarar 1970 zuwa 1985. A shekarar 1985 ne ta koma jami’ar Jos inda ta ci gaba da koyarwa har zuwa shekarar 1990. A halin yanzu ta yi ritaya , tana kuma zaune a garin Zariya.

Farfesa Gideon Tseja
Haka shi ma Farfesa Gideon Sunday Tseja aboki ne na kut da kut ga Dakta Bala Usman na tsawon shekaru. Ya yi karatunsa a jami’ar ABU Zariya da kuma wata jami’ar a Birtaniya ya kuma fara aikin malamta ne a jami’ar ABU a shekarar 1971 zuwa shekarar 2018 a hakin yanzu ya yi ritaya yana kuma harkar wallafa litattafai a garin Zariya.

Attahiru Bala Usman kwararrere ne a fannin kula da gurbacewar muhalli, ya kuma yi karatunsa ne a jami’ar ABU data Wales Cardiff a kasar Birtaniya. Ya kuma kasance daya daga cikin manbobin ‘British Safety Council’. A halin yanzu shi ne shugaban kanfanin ‘Allott (Nigeria) Limited’ wani babban kamfanin a Nijeriya.

Farfesa Usman A Tar
Farfesa Usman Tar kwararre ne a banagren kimiyyar siyasar duniya da kuma harkar tsaro ya kuma taba zama shugaban cibiyar ‘Defence Studies and Documentation’ haka kuma jigo ne a cikin kungiyar nan mai gudanar da bincike kan rayuwar alu’umma na Afrika. Ya kuma yi aikin koyarwa da bincike a kasashe da dama.

Hadiza Bala Usman
Hadiza Bala Usman ta yi karatunta ne a jami’ar ABU Zariya da kuma jami’ar Leeds ta kasar Birtaniya. Ta samu yabo da dama a kokarinta na bunkasa ilimin ‘yan mata da manyan mata. A halin yanzu ita ce shugabar hukumar kula da tashoshin ruwa na Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here