FARMAKIN GIDAJEN MARI: KADA FA A YI KITSO DA KWARKWATA

0

FARMAKIN GIDAJEN MARI: KADA FA A YI KITSO DA KWARKWATA

———————
Daga Bashir Yahuza Malumfashi
——————–

A ‘yan kwanakin nan, hukumomin tsaro sun shiga samame a makarantun da ake kira da GIDAJEN MARI, inda suke kama malamansu, suna sakin matasan da aka killace, ake masu gyaran halaye tare da koya masu karatu.
*
An fara da wata makaranta da ta shahara a Unguwar Rigasa, Kaduna. Daga nan aka tafi Daura Jihar Katsina. Nan ma aka farmaki irin wannan makaranta, wacce dad’ad’d’a ce kuma an dad’e da sanin yadda take gudanar da aikinta na killace kangararru. Daga nan kuma sai ‘yan sanda suka tafi Unguwar K’ofar Marusa a garin Katsina. Nan ma suka fafari shahararriyar makarantar MALAM NIGA, wadda ta dad’e tana gudanar da aikinta na gyara rayuwar kangararru.
*
Abin takaicin kuma shi ne, yadda aka ruwaito Shugaban K’asa #Muhammadu_Buhari ya ba jami’an tsaro umurnin da su ci gaba da d’aukar irin wannan mataki a dukkan irin wad’annan gidaje na kangararru a ko’ina suke.
*
Ni a ganina, wannan mataki ba zai haifar wa al’umma d’a mai ido ba, kuma ana son yin kitso ne da kwarkwata. Ina zargin ana son sake jefa al’ummar Arewa cikin wani tashin hankalin ne, domin kuwa a lokacin da aka kashe irin wad’annan gidaje na mari, aka SAKO KANGARARRUN MATASAN DA KE CIKINSU ZIWA CIKIN AL’UMMA, to sai dai mu ce Allah kiyaye.
*
Ni a ganina, wannan wani makirci ne ake son ci gaba da k’ulla wa Al’ummar Musulmin Arewa ko ma Najeriya gaba d’aya. Me ya sa na ce haka? Ga wasu dalilai nan a tak’aice:
*
Tun da farko an raba mu da tsarin iliminmu na farko (Ajami), aka maye gurbinsa da Boko, tare da tsarin da ya raba mu da Allah da manzonSa.
*
Na biyu, an sanya rayuwarmu zuwa gwadaben karya, inda kowa ya gama karatun boko yake son aikin gwamnati. Wannan ma makirci ne babba na lalata ruhinmu da rayuwarmu.
*
Na uku, an lalata mana addini da gudanuwarsa, inda aka bi ta hanyoyin makirci aka HADDASA MANA RARRABUWAR KAI – Izala, Darika, Shi’a, Kala-Kato da sauransu. Da gangan aka yi haka domin kassara mu, kuma ga alama sun yi nasara.
*
Wannan hare-hare da ake kai wa gidajen mari, ina tunanin wani sabon makirci ne ake shirin kulla mana. Ke nan yaran da suka kangare, suka zama annoba ga al’umma, aka killace su domin gyara dabi’unsu amma yau ake son sako su cikin al’umma domin su haddasa sabuwar rigima. Dama ga Boko Haram, ga Masu Garkuwa da Mutane, ga talauci, ga jahilci ya yi wa al’umma kukumi.
*
Idan da gaskiya ake so, sai gwamnati ta sanya hannu, ta inganta irin wadannan gidajen mari domin ci gaba da gyaran dabi’un kangararrun yaran da ke ciki. AMMA INA!
***
ALLAH KAWO MANA AGAJI!

See also  NEDC FLAGG’S OFF 12.2 BILLION NAIRA ROAD, MEGA SCHOOL PROJECTS IN YOBE.

——————–
(C) #Bashir_Yahuza_Malumfashi
Asabar 20-02-1441 (Hijiriyya).
19-10-2019 (Miladiyya)
——————–

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here