WATA SHARI A DA AKAYI A SHEKARAR 1950 A KATSINA
Danjuma Katsina @Taskar Labarai
Wata takardar rahoto da na gani a kan wata shara’a da aka yi a cikin shekarar 1950 a lardin Katsina, ya nuna yadda aka dade ana kulle bakin wanda ake son ganin bayansa.
Na ci karo da rahoton a wasu dimbin takardun dana ke da iko akan su. Sai naga labarin yana da darasin da zai amfani masu tasowa, da wadanda shekarunsu ke tafiya, na boye suna da gari da kuma shekarar da abin ya faru don kare mutuncin zuriyar wadanda abin ya shafa wadanda yanzu haka suna da yawa da karfi da kuma mutunci a jihar
Katsina.
Takardar rahoto sirri ne da wani Bature ya rubuta ma sashen tattara bayanan sirri na hedikwatar jihar arewa ta lokacin ga labari daga cikin cikakken rahoton. Amma kamar yadda na ce, zan boye sunan gari da shekara da sunayen duk wanda abin ya shafa.
A tsakanin shekarun 1950 ne, a lardin Katsina wani ya matsa don ayi bincike akan wasu mutane guda biyu, manufarsa a binciken shi ne, daya daga cikin wanda yake son a bincika yana shigar masu hanci da kudundune, yana da guri kuma ana zargin ma yana masu kulle-kulle ga Turawan mulkin mallaka.
Binciken da yake son ayi shi ne a inda yake aiki wasu kaya sun bace wanda ake zargin ya karkatar da su ne. Mai son a yi binciken sai da ya sanya aka yi masa bincike mai zaman kansa aka tabbatar da aikata laifin wadanda ake zargi.
Daga nan sai ya matsa a yi binciken a hukumance, don aje kotu wanda in an tabbatar da laifin dole ne suje gidan yari kuma su biya kayan da ake zarginsu akai. Wanda wannan zai karya masu alkadari ke nan.
Mai son ayi bincike yayi nasara aka yi binciken aka kuma gabatar da wadannan mutane gaban kotun shara’ar musulunci.
A kotu babu shaida da masu gabatar da kara zasu kawo, don haka sai aka kawo zabin yin rantsuwa da alkuara’ani akan anyi laifi koko a’a.
Alkalin ya baiwa wadanda ake zargin zabi, zasu rantse da alkura’ani koko za su amshi laifinsu?
Daya daga cikin su ya amsa laifin Alkali ya yanke masa hukuncin zama gidan yari da biyan kayan da suka salwanta.
Shi kuma dayan wanda dama ya san shi ne ake son aga an kama shi da laifi, yace bai aikata ba ya amshi a bashi rantsuwa da alkura’ani.
A wancan lokacin a masallacin juma’a ake rantsuwa aka bari sai ranar juma’a aka zo da/shi ana gama salla liman ya bashi rantsuwar da yayi har sau goma sha biyu.
Masallacin baki daya ya dauka da sallallami bayan yayi rantsuwar abin ya dame shi ya fara neman fatawar malamai, mafitan abin da ya aikata wani malami ya bashi mafita yace ga abin da zaka rika aikatawa rantsuwar ba zata yi aiki akan ka ba. Farko tilasta maka aka yi na biyu ka rantse ne don ka tsira da mutuncin ka, tun da ma kai ake son ganin bayan shi a binciken nan da kaiwa kotu.
Ta bangaren wanda ya zuga ayi binciken daga lokacin ya samu lafiyar mutumin, bai kara yi masu shisshigi ba kuma bai kara zama barazana a gare su ba.
KARSHEN INDA ZAN IYA KAWOWA A RAHOTON KENAN
…………………………………………………………………..
Taskar Labarai, da’ yar uwarta The Lnks News jaridu ne dake bisa yana gizo da sauran shafukan sada zumunta ana samunsu a www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com lambar Kira da WhatsApp 07043777779.