AN JINJINA MA JARIDUN TASKAR LABARAI
………Alhaji salisu yusufu majigiri shugaban PDP
Daga taskar labarai
Shugaban jam iyyar PDP a jahar katsina kuma Dan takarar mataimakin gwamna a zaben 2019 da suke kalubalanta a kotun daukaka kara. Ya jinjinawa jaridun taskar da Kira gare su da su rike kambinsu na fadin gaskiya da bincike labari na Musamman da zai yiwa Al umma amfani.
Alhaji salisu yusufu majigiri na fadin hakan ne ziyarar Musamman da ya kawo ofishin na jaridun a ranar jumma a 1 /11/2019. Inda ya ga yadda suke gudanar da ayyukan su.
Majigiri ya kuma gana da ma aikatan Wanda ya nuna jin dadinshi yadda jaridun ke bunkasa.majigiri yace nasan Ofis din nan tun ana harkokin buga takardu da fotositat nayi farin cikin yadda naga yana ta bunkasa.
Yace nayi farin cikin da naga kwanakin baya kamfanin ya sanar da daukar wasu aiki yace wannan ba karamin cigaba bane.yadda har wasu zasu sami aikinyi a wannan lokacin da aiki ya zama jau
Majigiri yace shi da jam iyyar su ta PDP zasu baiwa jaridun duk wani hadin da goyon baya idan suna binciken su na gaskiya da neman sanin hakikanin lamurra.
Muna fatan duk abin da muka .karanta a jaridun taskar labarai ya zama bamu da shakku akansu.