ANYI WA MIJI DA MATA YANKAN RAGO A BATSARI.
Daga taskar labarai
A Daren jumaa 1/11/2019 wasu da ba a tantance ba, suka tsallaka gidan wani bawan Allah mai suna Basiru, mazaunin kauyen Duba dake yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.sukayi wa matarsa (Jamila) yankan rago sannan suka juya kansa Shima sukayi masa yankan rago duk wannan ya faru ne da misalin karfe 1:00 na dare ganin haka yasa Yan uwansu suka garzayo dasu babbar asibitin Batsari,domin ceto rayuwarsu, amma dai ita matar ta rasu.sai dai shi mijin nata bai mutu ba, ya tsira da yanka a wuya.
Da muka zanta dashi majiyyacin Basiru Duba ko akwai wata gaba ko sa’insa tsakaninsa da wani? Sai ya bayyana mana cewa akwai wani matashi da suke neman auren wata yarinya mai suna Marwamatu tare, Wanda ya sameshi cikin mutane yayi masa wasu kalamai Kamar haka; Basiru tsakanina dakai akan soyayyar Marwamatu sai dai in kashe ka ko ka ka sheni.don haka ka taka sannu domin ni bazan iya barmaka ita ba. Amma ni ban tanka masa ba. Kuma wannan ta faru kasa da mako daya kafin faruwar wannnan lamarin.
Da muka zanta da mutanen garin sun tabbatar mana cewa sun bi sawun mutanen da sukayi wannan aika aikan, amma sawun ya dawo cikin garin don haka suka yanke hukuncin cewa lalle mutanen da sukayi aika aikan nan yan cikin garinsu ne.