MATSALAR TAKARDU: TA KAWO JINKIRIN TABBATAR DA KWAMISHINONIN KATSINA
daga taskar labarai
Wasu bayanai da jaridun taskar labarai suka tabbatar shine, matsalar takardun kammala karatu ya kawo tsaiko ga majalisar dokokin katsina ta tabbatar da kwamishinonin jahar a yau.
Wasu yan majalisar sun tabbatarwa da jaridar nan cewa sun gano wasu da aka tantance takardun da suka gabatarwa majalisa suna bukatar Karin bincike don gudun kada aji kunya.
Wakilan jaridun sun ga takardun wasu wadanda aka tantance da ake takaddama akai.wani an tantance shi amma sunan dake ga takardun gama makarantar sa. Na firamare daban, na sakandare daban hakan ma na gaba sakandare.
Wasu kuma takardun suna bukatar bincike kafin a tabbatar da sahihanci su. Akan su wani Dan majalisar yace kila sai sun Nemi hukumar DSS ta taimaka masu da Karin bincike da gabatar masu da bayanai.
Yan majalisun sun tabbatar wa da jaridar nan cewa lallai an Nemi alfarmar su akan su tabbatar dasu don ko sun fara aiki gadan gadan don amfanin Al ummar jahar
Dan majalisar yace da muka shiga tattaunawa an yi muhawara sosai daga baya wadanda suka amince a sake bin tantance takardun kowa.sukayi rinjaye.wannan shine babban dalilin a bangaren yan majalisar jaha.