MIKE FARUWA A MAJALISAR DOKOKIN JAHAR KATSINA ..akan tabbatar da kwamishinoni.
Daga taskar labarai
A karon farko a tarihin jahar katsina kuma a tarihin dawowar dimokaradiyya Karo na uku, yan majalisar jahar katsina sun kafa tarihi
Tarihin da suka kafa kuwa shine a satin da ya gabata. Sunayen wadanda gwamnan katsina ya basu a matsayin su tantance su da kuma tabbatar da su don a basu mukamin kwamishina
Yan majalisun sun Kira duk wadanda aka bada sunayen nasu sun kuma gabatar da kansu gaban yan majalisar.
Amma yanzu sun Dage zaman majalisar zuwa 11/11/2019.ba su kuma Sanya wata Rana ta tabbatar da sunayen da gwamnan ya mika masu ba.
Wanda a tarihi irinsa shine na farko da ya faru. Abin da aka Saba dashi shine da zarar aka gama tantancewa sai kuma a fara aikin tabbatarwa
Taskar labarai tayi bincike na musamman akan me ke faruwa kuma minene dalilin wannan tsaiko.
Wasu dalilai da jaridar ta gano babu tabbacin da zasu iya zama gaskiya ana iya ce masu WAII WAI.
Bincikenmu ya tabbatar mana tun daren lahadi aka gidan kakakin majalisar yana ta amsar bakin Muhimmai kuma manyan mutane daga jahar kuma aka ana ta kus kus aka fahimci tabbatar da kwamishinoni yana cikin kala wa kala.in an dawo majalisar wayewar garin litinin.
Majiya mai karfi daga ganawar da kakakin majalisar yayi a daren lahadi ya tabbatar, mana da wannan zancen da ma wasu bayanan.
Da safiyar litinin yan majalisar sun iso da wuri kuma suka zarce ofishin kakakin majalisar can aka yi musayar kalamai, kamar yadda wata majiya a cikin taron ta tabbatar mana.yan majalisar basu shigo zauren majalisar ba sai da Rana tsaka.
Akan tace kwamishinoni abin da kawai yan majalisar sukace shine wasu dalilai da suke da alaka da yadda ake gudanar da aiki.akan haka an dage tabbatarwa zuwa wata Rana da basu saka ba.daga karshen zaman kuma suka dage zaman majalisar sai 11/11/ watau litinin mai zuwa.
Me ke faruwa ne a majalisar? Shine tambaya da binciken da jaridun taskar labarai keyi.