YADDA KABILANCI YA TARWATSA ZABEN KUNGIYAR MARUBUTA TA KASA (ANA)
Daga Abdurrahman Aliyu
Daga ENugu da akayi taron
Tun a shekarar 1981 ne aka samar da kungiyar Marubuta ta kasa wadda ke da rassa a kafutanin jihohin da ke kasar nan. Mulikin wannan kungiya ana yin sa ne tsawon shekar biyu kuma shugabanni za su iya yin zango biyu kafin su sauka.
Tun bayan kafa wannan kungiya ake gudanar da taron kungiyar na shekara-shekara a duk watan Oktoba. A bana wanda ya kasance taro na 38 da kungiyar zata gudanar an shirya yinsa ne a garin Enugu kuma taro ne da za a sake zaben shugabanni kasan tuwar wa’adin wadanda ke sama ya kare. An bayyana cewa a tarihin kungiyar ba a taba samun shekarar da mutane suka halarci taron ba irin wannan hakan ya biyo bayan ziyarce-ziyarcen wayar da kai da ‘yan takarkari suka yi zuwa jihohin kasar nan domin nuna muhimmancin kungiyar da kuma halin da shugabannin dake sama suka jefa kungiyar ciki, musamman na wawurar wasu filaye daga cikin filin da aka ba kungiyar domin gina sakatariya a birnin tarayya Abuja.
An fata gudanar da wannan taro ranar 31 ga wantan Oktoba a cikin Birnin Enugu inda tun a ranar aka fara fuskantar matsaloli na rashin tsari da kuma wariya da kabilanci daga jagororin shirya wannan taro. Musamman rashin bayar da masauki, rashin tarar mutane musamman wadanda suka zo daga Arewacin kasar nan, babu wani exco na kungiya da ya tare su ko ya yi murna da zuwansu.
Haka ma da gari ya waye ranar 1/11/2019 nan ma a baban dakin taro na kasa da kasa da ke IMT a birnin na Enugu babu wani jami’in kungiya da ya tarbi wasu baki. Haka ma a wajen gabatar da jihohin da suka halarci taron asai aka ki ambatar jihohin Arewa irinsu Katsina da Kano da Jigawa d Bauchi da sauransu, sai da mahalarta wadannan jihohi suka tayar da bore sannan.
A bangaren rahoton yadda aka kashe kudade nan ma an samu tirjiya bayan shugaban wannan Kungiya mai barin Gado Danja Abdullahi ya gama bayani inda aka kalubalance su da rashin bin doka da Oda na kashe kudade da kuma danniya da nuna wariya ga wasu Exco din, kamar yadda sakatarwn sa ya bayyana cewa bai san inda aka samo wadannan bayanai ba. A takaice dai shi Shugaban Danja Abdullahi shi ne ya zauna ya tsara kome da kansa shi yasa kuma kitsa yadda yake somzabe ya kasance, domin rufe almundahana da kuma kunbiya-kunbiyar da suka shirya.
A ranar 2/11/2019 ranar ne aka fitar domin yin zabe amma abin mamaki sai aka cigaba da wasa da hankalin mutane har sai karfe 8:00pm sannan aka fara kiran wakilai domin kada kuri’a amma da aka zo jihohin arewa sai aka rika kiran mutane kalilan duk kuwa da cewa ga mutanen da suka zo kuma suka biya kudi, amma sai ka rika kiran wadanda basu ma a wajen taron misali a Sokoto an kira Kabir Assada wanda bai halarci taron ba ma sam, a Kano kuwa cikin mutum 17 da suka halarta sai aka kira mutum bakwai kacal a jihar Katsina cikin mutum 20 da suka hakarta sai aka kira mutum daya kacal, amma a jihar Imo kadai sai aka kira mutum 45 sakamakon dan takarar da shi Denja ke son ya ci zabe a can yake, haka aka rika kiran jihohi kudu da tarin mutane amma jihohin arewa ba kowa wasu jihohin Arewar ma shi Denja cewa ya yi ba zasu yi zabe ba wai saboda basu taba halartatr taro a lokacin shugabancinsa ba jihohin sun hada da Kaduna da Bauchi da sauran su.
Wannan kama karyar da nuna wariya ita ta harzuka wasu daga jihohin arewa inda suka fara nuna bore da kin aminta da wannan kama-karya bayan da a gefe guda shima dan takarar da ya fito daga jihar Akwa Ibom ya tayarda bore na hana mutanen sa yin zabe da ake son yi duk da kasancewarsa sajataren kungiyar har zuwa ranar yin zaben amma bai san hanyar da aka bi aka samo wadannan suna ye ba.
Daga karshe dai waje ya hargitse an cigaba da rera taken rashin amincewa da kuma kira ga masu gudanar da zaben da su tabbatar da an maido wuta a wajen zaben, wanda hakan ya sa hukumar makarantar da ake zaben ta bada sanarwar gaggawa na cewar a fice mata daga dakin taro domin gudun haddasa hasara sakamakon rashin iya shugabanci da jagoranci na Denja Abdullahi.
Daga nan an kira zama na ‘yantakarar duka hudu domin tattauna matsaya, inda biyu suka aminta da yin zabe biyu kuma suka aminta da a daga, da aka kira babban mai bada shawara na kungiyar sai ya bada shawarar cewa, kundin tsarin kungiya ya zo da mqfitar cewa in aka samu irin wannan tirjiya to daga zabe za a yi.
Daga nan aka tattara shugabanin jihohi baki daya aka yi zama na musamman inda suka cimma matsayar a sake shirya zabe cikin kwana 180 kamar yadda kundin tsarin kungiya ya bayar, kuma aka zabi birnin Abuja a matsayin inda za a yi zaben.
Ko shakka babu wanann taro ya nuna gazawa da kuma kabilanci tare da son rai a fili ga tsohon shugaban wannan ku giya Malam Denja Abdullahi sakamakon wani abu dake zuciyar sa na son rai.