KYAWAWAN HALAYE GUDA HAMSIN (50) NA BABA MAMMAN DAURA; LALLE IRIN SU BABA MAMMAN DAURA SUN YI QARANCI A WANNAN ZAMANI ??
#JaridarRijiyarKusugu 11-11-2019
1. Baba Mamman mutum ne mai tawakkali ga Allah.
2. Mutum ne wanda bai damu da suka ko yabo ba.
3. Mutum ne mai godiya ga Allah da abin da yake da shi, bai damu da tarin dukiya ba.
4. Mutum ne wanda bai damu da mulki ko mukami ba.
5. Mutum ne wanda bai damu da nuna kansa a bainar jama’a ba.
6. Mutum ne wanda bai damu da sanya tufafi masu mugun tsada ba.
7. Baba Mamman ba mai son nuna yafi sauren mutane kyakkyawar dabi’a ba ne.
8. Baba Mamman ba mai saurin yanke hukunci ba ne a kan mutane.
9. Ba mai son nuna shi mai dukiya ba ne.
10. Ba mai wulakanta jama’a ba ne.
11. Mutum ne mai hakuri da juriya a kan abin da duk ya same shi.
12. Mutum ne mai yawan godiya ga Allah.
13. Mutum ne wanda bai wasa da ibadah.
14. Mutum ne wanda bai cika yawan yin magana ba.
15. Mutum ne mai fad’a wa diyansa gaskiya komai d’acin ta.
16. Mutum ne mai barkwanci a cikin iyalansa.
17. Mutum ne mai yawan yabon matarsa.
18. Mutum ne mai yawan yi wa matarsa kyauta.
19. Mutum ne wanda bai taba sakin matarsa ba.
20. Mutum ne wanda bai taba yi wa diyansa auren dole ba.
21. Mutum ne wanda bai da son kai.
22. Mutum ne d’an gargajiya wanda bai nuna mugun so a fili ga diyansa.
23. Mutum ne mai nuna damuwa idan wani ya shiga cikin damuwa.
24. Mutum ne mai yin wasa da diyansa irin wasannin al’adun Hausa/Fulani.
25.Mutum ne wanda idan bai jin wasa toh zai nuna maka cikin natsuwa ba tare da hauragiya ba.
26. Mutum ne wanda bai rungumar diyansa mata idan sun fara girma, ba kamar iyayen wannan zamani ba.
27. Mutum ne wanda bai nuna bambanci a tsakanin diyansa, yana yin adalci a tsakaninsu.
28. Mutum ne mai taimakon yan uwansa, diyan abokansa, dama wadanda bai sani ba ta hanyar daukar nauyinsu domin su yi karatu.
29. Mutum ne wanda ya kyautatawa iyayensa matuqa lokacin rayuwarsu.
30. Mutum ne mai kyautata wa masu yi masa aiki, inda mutuwa ce ko tsufa suke raba shi da su.
31. Mutum ne wanda bai ‘bata lokacinsa a kan abin da ba zai amfane shi ba kuma ba zai amfani al’umma ba.
32. Mutum ne wanda burinsa ya samar da kamfanoni domin mutane su samu aikin yi, ba don ya mallaki dukiya shi kadai ba.
33. Mutum ne mai yin aiki tukuru na tsawon awanni don ganin ya ci halal dinsa.
34. Mutum ne wanda ya fad’a wa diyarsa cewa, duk mutuman da ya sanya kudi da kuma mallakar abin duniya a gaba, toh mutuman nan ba zai ta’ba samun kwanciyar hankali ba.
35.Mutum ne mai gaskiya da rikon amana.
36. Mutum ne wanda bai son maha’inta.
37. Mutum ne wanda ya taba yin wani rubutu a kan Dakta Mamman Shata saboda basirarsa a fagen waka, amma sai ya fasa wallafa rubutun a kamfanin jaridarsu saboda ba ya son Dakta Mamman Shata ya yi masa waka.
38. Mutum ne wanda Sarkin Daura Muhammadu Bashar ya ba shi sarautar Durbin Daura, yanzu tsawon shekaru 25, amma ya ki yarda a nad’a shi, saboda gudun kar ya zamto mai jiji da kai.
39. Babban dan kasuwa ne mai fitar da haqqin Allah (Zakkah), wanda kuma bai ta’ba kin biyan harajin gwamnati ba, wannan ne ma ya sa gwamnatin jihar Kaduna ta karrama shi a wasu shekarun baya.
40. Mutum ne wanda gwamnati ta ta’ba ba su filaye a Abuja kyauta saboda wani aiki da suka yi wa kasa, amma shi ya ce baya so, ya yi wannan aiki ne saboda kishin kasarsa.
41. Mutum ne wanda matarsa ta ce, wani lokaci takan yi abin da zai bata masa rai da gangan don ta ga fushinsa, amma sai ta ga ya ki yin fushi, saboda tsananin kawar da kai a kan abu. Ka ji Maza kai!
42. Mutum ne wanda duk abin da wani zai yi mai na cutarwa sai ya ce a bar shi da Allah.
43. Mutum ne wanda idan lokacin Sallah ya yi sai ya cewa diyansa “Haramar Sallah”, sai duk a tashi a tafi domin yin Alwala a yi Sallah.
44. Mutum ne mai kiyaye dokokin Ubangiji iya-iyawarsa.
45. Mutum ne wanda yake rera wa diyansa wakar mawakin nan Narambad’a idan basu samu yadda suke so ba a wani lokaci a rayuwarsu, domin su fahimci yadda rayuwa take:
“Wata rana a sha zuma,
Wata rana a sha mad’aci,
Haka duniya ta ke”.
46. Mutum ne wanda bai sa’ba alkawari, idan zai yi, toh zai yi, idan ba zai yi ba, toh ba zai yi ba, zai fad’a maka gaskiya.
47. Mutum ne wanda bai son ka ta yayata shi idan ya yi maka abin alheri.
48. Mutum ne mai tsananin son sirri, maras son hayaniya.
49. Mutum ne mai tsananin kaifin basira wanda ya yi amfani da basirarsa wajen taimakon al’ummarsa.
50. Baba Mamman Daura, mutum ne mai saukin kai, wanda ya yi imani da Allah, ya kuma yarda da Qaddara mai kyau da maras kyau, ba kamar yadda wasu mutanen suka dauke shi ba.
Muna rokon Allah ya kara azurta mu da mutane irin su Baba Mamman Daura ??
#JaridarRijiyarKusugu 11-11-2019 ??