TSAKANIN LADO DA MASARI: KATSINA CE FARKO (1)

0

TSAKANIN LADO DA MASARI: KATSINA CE FARKO (1)

Daga Sharhin Taskar Labarai

Gobe Talata kotun daukaka kara ta kasa zata fara sauraren karar da jam’iyyar PDP ta daukaka a kan zaben 2019.

Zaben da APC ta tsaida Aminu Bello Masari PDP ta kuma tsaida Yakubu Lado Danmarke sakamakon zaben da INEC ta bayyana cewa Alhaji Aminu Masari na jam’iyyar APC ne yayi nasara.

A irin wannan yanayin da ake ciki babban abin da ya kamata mai kishin jihar ya kawo shi ne ajiye banbancin jam’iyya ya bijiro da jihar a gabansa.

Shin wanene yafi cancanta? Matsayin gwamnan babban matsayi ne, da ya fi karfin kace zaka ba wanda tarihin sa yake cike da labarai. Kar ayi kuskuren lokacin da ake neman canji ba a rika kawo Allah ba. Sai aka rika cewa cewa kota halin kaka, da canjin kuma yazo sai Allah ya bar jama’a da abin da suka nema.

Kujerar gwamna mai wukar yanka da cikakken iko ba karamin abu bane. Tarihi ya nuna mana inda gwamna ya rika rikici da ‘yan majalisu ba kwamishinoni ya rika yin abin da yaga dama don kawai ya wataya. Don haka, kar kace wai wasu ‘yan majalisu zasu iya taka wa gwamna burki.

Tarihi ya nuna mana yadda gwamna ya hana jiha zama lafiya da rarrabuwar kai da fadace-fadace da rikici da kashe-kashe don kawai shi ya zauna a bisa mulkinsa a matsayin gwamna.

Tarihi ya nuna mana inda ‘yan siyasa suna hawa zasu kakkabar da duk na tare dasu don karsu kawo masu cikas, kuma ba abin da zai faru. Kujerar gwamna wadda ake cewa mai cikakken iko ba karamin al’amari bane, wanda za a yi wasa da ita ba, kuma kowane biri boko ya kama ta ayi gangancin mika mai ita.

A halin da ake ciki a Katsina a gaban kotun koli muna da ‘yan takara guda biyu da suke gaban kotun. Jamiyyar canji ta APC wadanda sune ke a bisa mulki karkashin Alhaji Aminu Masari, da kuma Sanata Yakubu Lado.

Mu a jaridar Taskar Labarai duk jam’iyyun basu da matsala suna da abubuwa masu kyau kuma suna da nakasu, suna da mutanen kirki suna kuma da baragurbi.

See also  Za'a Fuskanci Mamakon Ruwan Sama A Wasu Jihohin Arewa

Mulkin jam’iyyar PDP a Katsina na shekaru 16 ya gina Katsina sosai kuma ya mai da ita ta tsere ma sa’a a cikin danginta.
A ra’ayin Taska Labarai a zaben 2019 ta tsaida dan takara da bai dace da jihar Katsina ba, nan ne in da tayi babban kuskure.

Dan takarar da yayi ciyaman a karamar hukumar sa an san kuma me ya faru yayi dan majalisar tarayya, mazabarsa basu manta da abin da yayi ba. Bisa wani tsari na siyasa aka bashi takarar sanata, daga nan ya zarce shima tarihi na killace rayuwarsa a sanata, ya taba tsayawa takarar gwamna shima dambarwar da aka shiga ba wanda ya manta da ita.

Dan takarar da duk iyalanshi da mahaifanshi ya kwashe zuwa wata jiha, wani ziyara da editocin jaridun suka kai a garin sun tabbatar baya da kowa, sai gidajen da suka Gina.

Dan takarar da bai fara gina gida a Katsina ba, sai da zai tsaya takara, kuma da yana kamfen bai taba kwana Katsina ba. Komin dare sai yaje jihar Kano can yake kwana da safe kuma ya wo sammako dan takarar da duk ibtila’in da jihar Katsina ta shiga na ‘yan ta’addan fulani bai taba fitar da sanarwa ta jaje ko alhini ba koda kuwa sadara daya ce, balle zuwa jaje. Dan takarar da hatta uban gidan nashi a siyasa bai taba raka shi kotu ba don jajanta masa.

Dan takarar da shima yana da abin da za a gabatarwa a kansa a kotun kasa kuma ayi shari’a in Allah ya bada sa a ayi nasara. Taskar labarai da bayanai birkin akan dan takarar na tabbacin cewa ganganci ne a mika masa lamarin jiha kamar Katsina.

Don haka Al’ummar Katsina, ya kamata jihar ta zama ita ce farko a wajensu, kuma ya kamata su dau casbahar kar Allah ya jarabce su da kawo masu dan takarar da zai tsaida hannun agogo chak.
________________________________________________
Jaridun taskar labarai da the links news jaridu ne masu zaman kansu dake bisa yanar gizo da sauran shafukan sada zumunta. Suna a www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com layin Kira ko whazzap 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here