DR ZAHRA’U MUHAMMAD UMAR XIN DA NA SANI

0

DR ZAHRA’U MUHAMMAD UMAR XIN DA NA SANI


A kullum Bahaushe yakan ce xan’adam tara yake bai cika goma ba musamman in aka kalle shi ta vangaren yau da kullum amma Anty Zahra’u kamar yadda muka taso tun a makarantar W.A.TC Goron Dutse za mu iya kiranta ta cika goma cif har da xoriya.
Zan fara da sanina da ita lokacin da aka kaini makarantar sakandire ta WATC Goron Dutse a lokacin Anty Zahra’u tana aji huxu a makarantar. Tun daga ranar da na fara ganinta na tabbatar da cewa wannan uwa ce don kuwa yadda tun tana aji huxu hukumar makarantar ta jingina tarbiyyar xalibai da kula da walwalarsu musamman sababbin xalibai. Sakamakon yadda ta riqe xalibai da amanar da ta nuna da qoqarinta da jajircewa hukumar makarantar ta tabbatar da ita a matsayin shugaban xaliban (Head Girl) A wannan lokacin Anty Zahra’u ta tsaya tsayin daka ganin walwalar xaliban da duk wani abu da ya shafe su tamkar uwa da uba na tattare da su. Komai dare ba ta jin tsoron ta fito ta zagaya makarantar don ta tabbatar da tsaro . Ba na mantawa a lokacin xalibai na kukan wani na leqowa yana ba su tsoro ga kuma masu gadi suna qaryata qorafin xaliban. Don haka suka kai kuka gurinta. A washegari ita kaxai ta je ta tsaya a wajen ta hana xalibai zuwa wajen ta ce su yi wa mai leqowar qofar rago. kuma cikin yardarm Allah ita ta kama mutumin sannan ta sa aka kira masu gadin. Wannan jarumtar da nuna ba qaramin kankaro martabar makarantar ta yi ba. Tun daga lokacin muka tabbatar da kishinta ga ‘ya’ya mata.
A Hostel lokacin da babu aji akwai lokutan da takan ware musamman saboda yin nasiha a kullum abin da nakan tuna a nasiharta shi ne na yadda mace za ta zama mace ta gari a gidansu wajen yi wa iyaye da ‘yan’uwa biyayya da yadda za ta yi bayan an yi mata aure da ma yadda za ta riqe ‘ya’yanta har su yi alfahari da ita. Tsafta da ladabi da tsoron Allah a kullum shi ne kanu mafi xaukar lokaci ana yin sa. Sannan bayan an kammala duk mai wata damuwa yakan faxa mata damuwar nan kuwa ko dai a harkar karatu ko a matsalar gida ko kuma a tattalin arziqi duk wanda ya kai wannan kukan wajenta sai ta bi duk yanda za ta yi don share masa hawaye. Abin mamaki a lokacin ita kanta shekarunta ba su taka kara sun karya ba, sai dai Allah ya yi mata baiwa ta iya shugabanci da tallafar ‘ya’ya mata da iya tsara Magana mai kwantar da hankali.
Haxuwarmu da muka yi da ita lokacin muna karatun digiri na xaya ni da ita a jami’ar Bayero ta Kano ban yi mamakin yadda ta zame wa xalibai abokanan karatunta uwa ba. Don kuwa akwai lokaci da ta ware musamman don warware duk wata maslaha da ta shafi addini da zamantakewar aure haka in har kana da matsala wadda ba ta shallake aljihunta ba za ta yi.
Lokacin da take koyarwa a Makarantar ‘yanmata ta W.AT.C Goron dutse ta tarbiyyar xalibanta kamar a wuyanta ita kaxai aka rataya su.Ta xauki xalibai mata tamkar ita ta haife su motsinsu da damuwarsu da buqatunsu ta sa su gabanta kuma tana tsaye. Kullum maganarta malami da iyaye suka kawo wa amana ba iya koyarwa ce aikinsa ba har da tarbiyya da saita masa rayuwa duk na wuyan malami Wannan ta sa ko aure xaliban za su yi sukan gayyace ta gayyata ta musamman don ta ba su lacca kan zamantakewar aure. A nasiharta a kullum takan qara musu da ba ta son zaman kashe zani wajibi ne duk renonta ya tabbatar yana da sana’a. Wannan faxakarwar ta shiga ruhin xalibai mata da yawa da suka tashi qarqashinta sun zama masu abin yi. Lokacin da ta bar W.AT.C Goron Dutse ta koma Makarantar Turasu duk da haxaka ce mata da maza wannan bai hana ta xorawa daga inda ta tsaya ba na fifita mata da zame musu linzami a rayuwarsu.
Zamanta malama a makarantar kwalejin Malam Aminu Kano wato Legal nan ta koma alqali kuma mai bayar da shawara wato colsultant don kuwa duk wata mai matsala ko dai da miji ko abokiyar zama ko mai shirin aure nan za ka ji xalibai kai tsaye na faxin “a je wajen malama Zahara’u” . Anty Zahra’u ta sha haxa ma’aurata ta yi musu sulhu kuma Allah ya yi mata baiwar in har ta yi sulhun duk wanda ta ba wa laifi shi ne mai kuskuren kuma ba zai kuma maimaitawa ba don kuwa yadda za ta yi masa nasiha in wani abu ne da ya shafi magani za ta xau nauyi in abin da ya shafi jari ne ko kuma wani ne a tsakani yake janyo rashin jituwar kamar uwar miji ko dangin miji duk za ta je da kanta ta warware matsalar.
Ga duk masu zuwa aikin hajji sun san malama Zahra’u da irin gudunmawar da take bayarwa wajen wayar da kan mata a kan duk abin da ya shafi mas’alolin Hajji komai dare ko da kuwa bacci take sai an tashe ta ta bayar da fatawa. Don haka in wata matsala ta faru an dinga neman malama Zahara’u kusfa-kusfa don samun nutsuwar ibada. Mahajjata mata daga Kano tun a wajen bita suke shaida qoqarinta.
Cancantarta da yadda take xaukar larurar mata da karvo musu ‘yancinsu da yadda ta kware wajen nemawa mata mafita a duk rayuwarsu kama daga ta zamantakewar aure da sana’a da lafiya da ilimi ya sa gwamnan Kano na wancan lokacin ya ga dacewar ya ba ta mataimakiyar shugabar Hisba. Sanin kowa ne Matsalolin Hisba kashi saba’in cikin xari na mata ne. Ko anan Anty Zahra’au ba ta ba wa marar xa Kunya don duk matsalar da ta zo gidan Hisba sai ta ga bayanta. Ba wannan ne abin burgewa ba yadda za ta dinga bibiyar abin da tabbatuwar xorewarsa shi zai fi ba da mamaki. Duk mai mu’amala da hisba ya san yadda ta xau ragaman duk ma’aikatan da ke qarqashinta da matan da ake kawowa .
Ba abin mamaki ba ne don malama Zahara’u ta riqe amana don tun tasowarta nasiharta ga mata su riqe amanar mazajensu. Batun amanar da ta riqe ta abincin ‘yan gudun hijira na zunzurutun kuxi har miliyan ishirin wanda Aminu Xantata ya ba ta bai zama abin da za a tattauna ba don tunda ta tashi a cikin riqon amana take ta dukiya da kayan dukiya da kuma ta ‘ya’yan al’umma. Komai ta yi shi a bayyane ba tare da qunbiya-qunbiya ba wannan ya sa duk wanda ke cikin aikin ciyarwar ya san yadda aka yi aikin. Wani abin a yabawa na amana da Dakta Zahara’u ta yi shi ne riqe ‘yan gudun hijira da kula da su na mutane 370. Wannan ba qaramin qoqari ba ne ta kula da su ta saita musu rayuwa, ta samar musu abin yi wanda da dama sun gwammace zamansu a hannunta fiye da inda suka fito. A vangaren yara qanana kuwa Dakta Zahra’u ta yi rawar a gani a yaba yadda ta yi hanyar xaukar nauyin yara guda 121 a makarantun kuxi tare da jagorancin biya musu kuxin. ‘Yaran nan marayu ne da marassa qarfi ‘ya’yan talakawa kuma abin birgewa ba ma ta san yadda ake biyan kuxin ba, kawai ta haxa su da masu makarantar wadda mai xaukar nauyin kai tsaye da makarantun suke magana. Kawai aikinta shi ne bibiya ta tabbatar da yaran suna karatun a makarantun.
Lallai Maigirma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi hangen nesa wajen nemawa matan jahar Kano mafita da share musu hawaye kamar yadda masana ke cewa ba a tava samun kwamishiniyar mata da ta dace da ofishinta kamar Dakta Zahra’u Muhammad ba saboda tun da ta kai shekara goma sha xaya a duniya ta fara yi wa mata hidima jininta da tsoka da ruhinta da lafiyarta. Har zuwa yau da aka danqa mata matan Kano Dr Zahra’u Muhammad ba ta numfasa ba.
Halayenta na Rashin girman kai da fara’a a duk inda ka ganta da Gaskiya da zama kaifi xaya. In kuwa ka ga fushinta to cikin uku ne ko dai an kaucewa wani abu da ya shafi addini ko rashin Gaskiya ko ta ga mace sakarai da ba ta son ciwon kanta ba. Fatanmu Allah ya sa ta shiga Ofishinta a sa’a, halayenta na gari da ta faro tun daga yarinta Allah ya qarfafeta ta ci gaba da aiwatar da shi.
Matan Kano suna Godiya don an ajiye kwarya a Gurbinta!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here