KILA YAU A KAI ABDULMUMINI SHEHU SANI KOTU..

0

KILA YAU A KAI ABDULMUMINI SHEHU SANI KOTU……
Daga taskar labarai
Taskar labarai ta tabbatar da cewa a jiya laraba 13/11/2019 hukumar yan sanda suka tafi da Abdulmumini shehu sani shugaban jam iyyar NCP.
Sun tafi dashi ne akan wani taron manema labarai da ya yi a karshen satin da ya wuce inda a taron ya zargi cewa gwamnan katsina Alhaji Aminu Bello masari ya yi yunkurin bada Toshiyar baki ga daya daga cikin alkalan da sukayi shara ar zabe a jahar katsina.
Taron manema labaran da Abdulmumini shehu sani ya gabatar da wani rasidi maras tabbacin ina aka samo shi? waya rubuta shi?waya bayar ?kuma waya amsa?
Taron manema labaran da wasu kafofin labarai sukayi amfani da bayanan da akayi a wajen suka bada labarinsu.
Wakilan taskar sunje hedkwatar yan sanda inda suka tabbatar yana a wajen tsare, kuma aka tabbatar masu ana daukar jawabinsa don duba yiyuwar kaishi kotu a yau.
Shi dai shehu sani ya zargin cewa wai wannan rasidin maras tabbas, wai kudi ne na yunkurin bada Toshiyar baki Wanda yace gwamnan katsina Aminu Bello masari yayi yunkurin badawa.
Akan haka wasu masoya gwamnan suka shigar da koke akan yan sanda suyi bincike da kaiwa kotu don zakulo da tabbatar da gaskiya lamarin.
Bisa waccar takardar korafin da aka ba yan sanda ne, suka kama Abdulmumini shehu sani suke kuma bincike
Duk kokarin jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda yaci tura.wakilan taska sun je Ofis din sa bayanan. Sun kuma aika masa sakon wayar hannu babu amsa.
________________________________________________
Taskar labarai jarida ce mai zaman kanta dake a www.taskarlabarai.com da kuma yar uwarta the links news dake a www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta. Kira ko whazzap 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here