REMIUM TIMES za ta maka DANA AIR, Blueprint da Daily Nigerian

0

Kamfanin jaridar PREMIUM TIMES ta yanke shawarar maka kamfanin sufurin jiragen sama na DANA AIR da jaridun Blueprint da Daily Nigerian kotu, saboda kazafin da su ka yi ma ta cewa ta buga wani labari, alhali ba ta buga ba.

A ranar 4 Ga Nuwamba ne suka buga labarin cewa Hukumar Kula da Sararin Saman Najeriya ta hana jiragen Dana Air zirga-zirga.

Bayan wani lokaci kuma sai su ka karyata kan su da kan su, su ka ce labarin ba gaskiya ba ne. Sannan su ka cire labarin a shafin su, tare da cewa su ma daga shafin PREMIUM TIMES suka dauko labarin.

Kamfanin DANA AIRLINE ya rika yin cacar-baki da PREMIUM TIMES, ya na ikirarin cewa jaridar a ranar 4 Ga Nuwamba ta buga labarin karya a kan kamfanin. Hakan a cewar Dana Airline ya zubar wa kamfanin da kima. Har ma ya yi barazanar maka wannan jarida kotu.

Mu na kara nanatawa da babbar murya cewa PREMIUM TIMES ba ta buga wani labari a kan kamfanin DANA AIRLINE ba a ranar da suka yi ikirari ko kuma wata rana kusa da wannan.

See also  MA'AIKATAN KOTUN DA AKE ZARGIN DA YAUDARAR CIF JOJIN KATSINA:AN GABATAR DA SU KOTU

PREMIUM TIMES dai ta taba buga labari tun a ranar 5 Ga Yuni, 2012, cewa Hukumar Kula da Sararin Saman Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar DANA AIRLINE, bayan da wani jirgin kamfanin ya yi hatsari inda dukkan fasinjojin 149 da ke ciki su ka mutu.

Tun daga wancan labarin har yau ba mu kara buga wani labari dangane da DANA AIRLINE ba mai kama da shi.

Don haka za mu garzaya kotu domin bin hakkin bata mana suna da DANA AIRLINE da wadancan jaridu suka yi, ta hanyar tattago wani tsohon labari tun na 2012, daga rumbun ajiyar tsoffin labaran mu, suka buga shi a matsayin sabon labari.

Sannan kuma mu na kalubalantar su da su kawo inda su ka ce mun buga labarin, wanda mu dai ba mu buga ba.

PREMIUM TIMES ta na nan kan turbar da ta ke a kai kan buga sahihan labarai. Ba kuma za ta taba kaucewa a kan wannan sahihiyar hanyar buga ingantattun labarai ba.

Sa Hannu:
IDRIS AKINBAJO
MANAJAN EDITA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here