ALHAJI DAHIRU MANGAL YA ZAMA CON

0
2781

ALHAJI DAHIRU MANGAL YA ZAMA CON

Daga Taskar Labarai

Mun samu tabbacin Alhaji Dahiru Bara’u Mangal ya samu lambar karramawar nan ta kasa ta CON a matsayin dan kasuwar da ya assasa kasuwancin da ya taimaki jama’a da kuma tattatalin arzikin kasa.

Wannan lamba ta CON girmamawa ce ta kasa wadda a kan baiwa wadanda suka cancanta bayan wasu sun gabatar da sunansu cewa sun cancanta Najeriya ta karrama su.

Daya daga cikin editocin jaridun Taskar Labarai da The Links na gaba-gaba wajen bada sunayen ‘yan jihar Katsina wadanda suka cancanta. Kuma su bi don su tabbatar cewa sun samu.

Lambar CON tana daya daga cikin manyan lambobin girmamawa koda a cikin jerin wadanda gwamnatin tarayya ke bayarwa.

A tsari shugaban kasa da kansa kan bayar da lambobin ga wadanda suka cancanta in lokacin bada su yayi.

Taskar labarai na kyautata zaton wasu ‘yan Katsina ma za su samu wasu lambobin na girmamawa domin sunayensu da tarihin rayuwar su na can ana tantancewa.

Muna taya Alhaji Dahiru Bara’u Mangal CON murna Allah shi kai mu lokacin amsa lafiya.
____________________________________
Jaridar Taskar Labarai jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma yar uwarta turanci mai suna The links news a www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta. 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here