YAU AN GABATAR DA SHEHU SANI KOTU
daga taskar labarai
Yau an gabatar da shugaban jam iyyar NCP Malam shehu sani a kotu majistire dake Kan titi sir Usman Nagogo a katsina
A zaman kotun na yau alkalin ya kori karar a yadda suka gabatar a zaman da ya wuce akan cewa ba a gabatar da ita yadda ta dace ba don haka ya sallami Wanda ake tuhuma.
Amma nan take masu shigar da karar suka ce sun sake tsarin yadda zasu sake gabatar da karar kuma sun sake shigar da ita.Anan take aka sake kiran karar kuma aka karanta tuhumomin akan cewa ana zargin sa da kiran taron manema labarai da bata sunan gwamnan katsina da kuma yada labarin a shafin sa na Facebook
Bayan karanta tuhumomin sai lauyan shehu sani ya Nemi a bashi beli inda anan take lauyan masu shigar da kara ya ce bai amince ba.bayan dogon muhawara alkalin ya daga shara ar zuwa ranar 5 ga watan disamba,domin ya bayyana matsayinshi akan ko zai bada belin shehu sani koko a a ?
Domin alkalin yayi muhawarar cewa tuhumar da ake ma shehu sani kotunsa bata da hurumi akansu.don haka ba zai iya cigaba da shara ar ba sai ya samu shawara.kuma bai iya bada belinshi sai babbar kotun tarayya.
Ana gama shara ar bata suna sai shehu sani ya sake tsayawa don wata karar wadda ake yi tsakanin shi Alhaji sani danlami tsohon Dan majalisar tarayya yanzu kuma kwamishinan matasa da wasanni .
Ita ma alkali yace a ajiye Wanda ake tuhuma a gidan yari har zuwa lokacin da za a dawo wa.
Kotun ta samu wakilai Wanda shugaban jam iyyar PDP Alhaji salisj yusufu majigiri da Alhaji salisu lawal uli da wasu yan jam iyyar PDP da kuma shugaban kungiyar jam iyyun siyasa da yan jarida