AN KWACE FILIN SARKIN KANO NA NAIRA MILIYAN 250 AN BASHI NAIRA MILIYAN HUDU.

0

AN KWACE FILIN SARKIN KANO NA NAIRA MILIYAN 250 AN BASHI NAIRA MILIYAN HUDU.
Daga taskar labarai
Gwamnatin jahar Kano ta kwace wani filin sarkin Kano Muhammadu Sanusi 11 da ya saya tun a shekarar 2010 a kudi naira miliyan dari biyu. 200.aka biya shi diyyar naira miliyan hudu da Rabi
Jaridun Daily Nigeria da Kano focus sun ce binciken su ya gano masu cewa anyi ma filin kudi darajar naira dari biyu da hamsin.kuma sarkin ya sayi filin ne tun a 2010.
Gwamnatin tace ta kwace filin ne, don a yi aikin hanya a bisa filin kuma sunyi tsammanin sarkin zai ba gwamnatin jaha filin kyauta don ayi aikin hanyar amma yaki don haka sukayi ma filin farashi kuma suka biya shi
Da za a kwace filin gwamnatin jaha ta kawo yan daba rike da miyagun makamai a filin suna ihu da bugun mutane.
Sannan kwamishinan ayyuka na jahar ya fara rusa kantanagar harabar filin da kansa.kuma gwamnatin ta tilastawa sarkin sai ya turo wakili da zaya shaidi yadda aka rusa katangar harabar filin, sarkin ya turo hakimin Garko Wanda gabanshi akayi komai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here