DALIBAN DA GWAMNATIN JAHAR ZAMFARA TA DAUKI NAUYIN KARATUNSU, SUN SAUKA KASAR SUDAN!
Cikin Iyawar Allah Dalibbai Hamsin da gwamnatin jahar Zamfara ta tura kasar Sudan domin karatun ilimin Likitanci da aikin Jinya sun sauka kasar Sudan lafiya lau. Insha Allahu nan gaba Kadan Sauran dalibbai 150 za su tashi zuwa kasar China, Cyprus, da India.
Kuma alhamdulillahi sun samu turbo mai kyau daga kasar Sudan din kamar yadda ku ke gani.
Allah ya sa wadannan dalibbai su amfani jahar Zamfara da Al’ummarta baki daya. Allah ya sa su zama jakadun Kirki a kasar Sudan din.
Abdulmalik Saidu Maibiredi
Senior Special Assistant to the Executive Governor Of Zamfara State
3nd December, 2019