ZUWA AIKI CIKI LOKACI A KATSINA

0
311

ZUWA AIKI CIKI LOKACI A KATSINA
Yau laraba 4/12/2019 wata hidima ta kaini hukumar kula da asibitocin jahar katsina, wani lamari da ya burge ni, shine yadda ma aikatan hukumar suke ta isowa aiki da wuri suna kuma sa hannu a littafin aiki na ma aikata wajen .
Dai dai lokacin da na isa, na iske shugaban hukumar dakta Abduljalil umaru Abdullahi, shima yana akan layi , Wanda ya Riga shi ya sa hannu shima ya bi kamar yadda kowa keyi.
Abin ya burge ni har na dauke shi hoto.Na bishi har Ofis naga wasu na jiran isowar shi, yana gama kimtsawa yace ma sakataren sa. A shiga a tsarin Wanda ya fara zuwa.
Zuwa aiki cikin lokaci na daga ciwon dake damun wasu hukumomi da ma aikatun katsina da kanana hukumomi. Kuma gwamnati bata kallon wannan bangaren .
Danjuma katsina , shine mawallafin jaridun The links news da jaridar taskar labarai dake a www.thelinksnews.com da kuma www.taskarlabarai.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here