Dubun Wani Matashi Mai Damfara Ta Hanyar Bank Alert na Karya Ta Chika a Katsina.

0

Dubun Wani Matashi Mai Damfara Ta Hanyar Bank Alert na Karya Ta Chika a Katsina…

Rundunar Yansandan Jahar Katsina tayi Nasarar Chafke wani Matashi da ya kware wajen Damfarar Yan kasuwa ta hanyar Tura masu da sakon ALERT na ‘karya a yau dai ne 10/12/2019 da misalin karfe biyu na Rana, bisa rahotannin sirri, Rundunar yansandan tayi Masarar Damke wani Matashi mai suna Musa Isah, Dan kimanin shekaru Talatin 30 a Duniya Mazaunin Unguwar Kwado, Katsina.

Shi dai wannan Matashi ya shahara wajen Damfarar Yan kasuwa masu shaguna ta hanyar tura masu da sakon banki na karya bayan yayi sayayyar kayansu.

Rana dai ta Bachi ne ga Matashin lokachinda yaje sayayya a shagon Alh Adamu Rabi’u, dake unguwar Kwado a nan Katsina, inda ya yaudari mai shagon ya amshi wasu Kofofi samfurin kirar kasar Chana wadanda kudinsu yakai kimanin N57,000:00k ya kuma tura mashi da sakon Banki na karya.

See also  Kotu Ta Daure Wani Dan Kasar China Shekara Biyar A Gidan Gyaran Hali.

A yayin binchiken Yansanda wanda ake zargin ya tabbatar da laifinsa inda ya bayyana cewa yayi makamanchiyar irin wannan yaudarar a wurare daban daban na Dubban Nairori a cikin garin katsina.

Haka nan ya bayyana cewa kimanin wata biyu da suka gabata yaje ya karbi Generator daga Abbas Plaza Katsina wanda kudinshi sun kai N120,000:00k suma yayi masu sakon Banki na karya.

Sai kuma Al-Ihsan Great Infinity Boutique inda suma yaje ya kwashi kayan sawa na kimanin N21,000:00k suma dai yayi masu sakon Banki na karya wato fake Alert.

Haka nana ranar 5/10/2019 yaje shagon Alh. Alin Kwai, dake bakin kasuwar Chake bisa titin, Kofar Guga Katsina, inda ya karbi buhunnan shinkafa, Man Olga da Macaroni wanda kudinsu yakai N65,000 suma ya tura masu fake bank SMS alert.

Yanzu haka dai Jamian tsaron Yansanda na cigaba dayin binchike.
Mun Ciro daga HK tv online

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here