MUMMUNAN HADARIN MOTA YA CI RAYUKA 25 A JIHAR BAUCHI

0
491

MUMMUNAN HADARIN MOTA YA CI RAYUKA 25 A JIHAR BAUCHI

Daga Maje El-Hajeej Hotoro

*22 sun taho ne daga jihar Katsina zuwa Yola
*4 sun taho ne daga jihar Bauchi zuwa Kano
*An kasa gano ‘yan uwan mamatan

Rundunar ‘Yansandan jihar Bauchi ta sanar da faruwar mummunan hadarin yau Alhamis a kauyen Gubi a hanyar Bauchi zuwa Kano. Hadarin da ya lankwame rayuka 25 motoci biyu ne Toyota Hummer mai dauke da Fasinjoji (22) sai kuma motar bas kirar J5 mai dauke da Fasinjoji (4) da shanu (20).

Motocin sun yi taho-mu-gamu wanda hakan ya janyo Fasinjoji (26) sun yi mummunan rauni.

Likitocin asibitin kwararru na Abubakar Tafawa Balewa sun tabbatar da rasuwar Fasinjoji (25) yayin da (1) ya jikkata.

Bincike ya tabbatar da cewa gaba daya Fasinjojin motar Toyota Hummer an dauko su ne daga jihar Katsina zuwa Yola yayin da Fasinjojin J5 kuma daga Bauchi suke zuwa Kano.

Sai dai abin takaicin mutum 4 ne aka iya gano danginsu yayin da ragowar mamata 21 ba a gano danginsu ba. Don haka ake rokon jama’a da su yada sakon nan ko za a dace.

DSP KAMAL DATTI ABUBAKAR
POLICE PUBLIC RELATIONS OFFICER
FOR: COMMISSIONER OF POLICE
BAUCHI STATE COMMAND

A KULA (Hoton Motocin Ba Na Hadarin Ba Ne An Sa Ne Don Isar Da Sako)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here