MURNA DA ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWAR ANNABI MUHAMMADU (S.A.W).

0

MURNA DA ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWAR ANNABI MUHAMMADU (S.A.W).

Daga Mohammed Bala Garba, Maiduguri.

HAIHUWAR ANNABI (S.A.W).
An haifi Shagabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W) a ranar Litinin, cikin watan Rabi’ul Awwal. Malamai sun qara wa juna sani game da kwanan watan da aka haife shi. Wasu suka ce: Biyu ga wata Rabi’ul Auwal, wasu kuma suka ce: Takwas ga watan, wasu kuma: Goma ga watan,w wasu kuma suka ce: Sha biyu ga watan.
Babban malamin Tafsirin nan, wato Xan Kasir ya ce: “Maganar da babu savani akai, ita ce cewa: An haife shi ne shekarar da ake kira shekarar Giwaye.” kamar yadda Ibrahim Xan muzir Alhuzami (malamin Bukhari) da Khalifatu Xan Khayyad da sauransu suka fada. Masana Tarihi suka ce: Lokacin da mahaifiyar Annabi (S.A.W) Nana Aminatu (R.A) ta xauki cikinsa ta ce: “Ban ji nauyinsa ba kamar yadda sauran mata suke ji, lokacin dana haife shi kuwa, sai wani haske ya fito tare da shi wanda ya haskaka gabar da yamma.”
An karvo hadisi daga Irbad Xan Sariya ya ce: “Na ji Annabi (S.A.W) yana cewa: Lallai haqiqa tabbas haka Allah ya rubuta a cikin Lauhul-mahfuz cewa ni ne cikamakin Annabawa, haka kuma al’amarin ya ke a gurinsa tun kafin a halicci Annabi Adam, abubuwan da suke nuna haka kuwa sune, Addu’ar mahaifina Annabi Ibrahimu (A.S) lokacin da ya roki Allah a aiko da wani Manzo cikin larabawa, da kuma albishirin da Annabi Isa (A.S) ya yi waw mutanensa cewa wani Annabi zai zo bayansa, da kuma hasken da mahaifiyata ta gani lokacin da ta haife ni, wanda ya haskaka qasar Sham (siriya).”
Mahaifin Annabi (S.A.W) ya rasu ne kafin a haife shi.Wasu malamai suka ce: Ya rasu ne bayan haihuwarsa da wata xaya ko kuma shekara xaya. Amma maganar da tafi shahara ita ce, ta farko.
SHAYAR DA ANNABI (S.A.W).
Suwaibah ce ta shayar da Annabi (S.A.W) zuwa xan wani lokaci, sannan aka nema masa wajen shayarwa a qabilar (Banu-Sa’ad), sai Halimatus Sa’adiyya ta cigaba da shayar da shi, ya kuma zauna tare da ita tsawon shekara hudu, a can ne ma aka tsaga kirjinsa aka tsaftace shi daga munanan halaye, ganin haka, Halimatus Sa’adiyya sai ta tsorata tayi gaggawar mayar da shi wajen mahaifiyarsa Nana Aminatu (R.A). Ita dai Halimatus Sa’adiya, ta kasance tana da ‘ya’ya kamar haka: Abdullahi, Anisa, Shaima’u. Ta samu albarka mai yawaw sakamakon renonsa da shayar da shi da tayi. Xaukewar fari da ya same su da su da mutanensu. Aminci a cikin al’ummarsu gaba xaya.
Ummu-aiman (baiwar da ya ci gadonta a gurin babansa.), ita ta cigaba da rainonsa bayan rasuwar mahaifiyarsa, sai kakansa Abdulmudxalib ya cigaba da kula dashi. Lokacin da Annabi (S.A.W) ya kai shekara takwas, kakansa ya rasu, amma kafin rasuwarsa, sai ya bada wasiccin riqon Annabi (S.A.W) wa Baffansa (wato Abu Xalib) sai ya cigaba da kula dashi, ya kuma bashi cikakkiyar kulawas da taimako da kuma goyon baya musamman ma lokacin da aka bashi manzanci, har takai da ya xauki xansa Sayyadina Ali yabawa Annabi (S.A.W) don ya taimake shi wajen isar da musulunci.
Mahaifiyar Annabi (S.A.W) ta rasu ne a hanyar dawowansu zuwa Makka a wani kauye da ake kirae (Abwa’i), a lokacin yana da shekara shida. Saboda haka ne ma lokacin da Annabi (S.A.W) ya zo wucewa ta wannan gurin zai nufi garin Makka shekarar da akayi (Fathu Makka), sai ya tsaya a gurin ya nemi izinin Ubangijinsa don ya ziyarci kabarin Mahaifiyarsa Nana Aminatu, Allah ya yi masa izini, sai ya tsaya ya yi kuka har yasa waxanda suke tare da shi kuka. kuma ya ce: “Ku ziyarci kaburbura domin tana tunatar da mutuwa.” Muslim ne ya ruwaito wannan hadisin.
Mahaifiyarsa ta rasu yana xan shekara shida, sannan sai kakansa Abdul mudxalib ya cigaba da renonsa, shi ma ya rasu Annabi (S.A.W) yana xan shekara takwas, wanda a sakamakon haka ne baffansa Abu Xalib (A.S) da kuma matarsa Fatimatu ‘Yar Asad (A.S) suka xauki nauyin renonsa.
Kasancewar gidan Abu Xalib yana da karancin yalwa, wannan ne ya sanya Manzo (S.A.W) ya motsa domin ganin ya xauki nauyin wannan gida, ta hanyar karbar kwadagon kasuwanci na fatauci kamar yadda yake al’amari sananne a wannan zamani.
AUREN ANNABI (S.A.W).
Annabi (S.A.W) ya auri uwar muminai Nana Khadija a lokacin yana da shekara Ashirin da biyar (25). Dalilin auren kuwa shi ne, Annabi (S.A.W) ya fita fatauci wa uwar muminai Nana Khadija zuwa qasar sham (siriya) tare da yaron gidanta Maisarah.
Bayan dawowarsu daga fataucin, sai maisarah ya ba wa uwar muminai Nana Khadija labarin abubuwan mamaki da ya gani game da Annabi (S.A.W), da kuma irin gaskiyarsa da riqon amanarsa, daga nan sai uwar muminai Nana Khadija ta nemi Annabi (S.A.W) da ya aure ta.
Abu Xalib (A.S) ya tafi wajan amminta Amru Xan Asad ya nemi aurenta ga Manzon (S.A.W), domin an kashe babanta kafin wannan lokacin.
Abu Xalib yana cewa a yayin da ya tafi neman aurenta ga Manzon (S.A.W), sai ya ce “Godiya ta tabbata ga Ubangijin wannan xaki (Na ka’aba), wannan da ya sanya mu daga tsatson Ibrahimu da kuma zuriyar Isma’il, sannan xan xan’uwana (yana nufin Manzon Allah (S.A.W)) ba a auna shi da wani mutum daga Kuraishawa a sikeli sai ya yi rinjaye, kuma ba a kwatanta shi da wani mutum sai ya fi shi xaukaka, ga shi yana sona Khadija, mun zo muna neman aurenta a wajanka, da yardarta da kuma umarninta, kuma sadakin yana kaina a dukiyata da zaku nema hannu da hannu ko kuma ajalan na rantse da Ubangijin wannan xakin na Ka’aba (wannan aure) rabo ne mai girma, addini mai yaxuwa, kuma ra’ayi cikakke” sai aka xaura aure.
Haka auren ya kasance, aka kafa gida mai haske cike da shiriya. Manzon Allah (S.A.W) yana fadi game da Khadija cewa ta yi imani da ni yayin da mutane suka qi ni, ta gaskata ni yayin da mutane suka karyata ni, ta taimake ni da dukiyarta yayin da mutane suka hana ni, kuma Allah ya arzuta ni da ‘ya’ya da ita ya hana ni ‘ya’yan mutane (ta wata matar).
Annabi (S.A.W) bai qara aure ba har zuwa rasuwar uwar muminai Nana Khadija, ta rasu ne kafin a yi hijira zuwa Madinah da shekara uku. Bayan rasuwarta, sai Annabi (S.A.W) ya auri uwar muminai Nana Saudah ‘yar Zam’an, sannan ya auri uwar muminai Nana Aishah ‘yar Sayyadina Abubakar, (ita kaxai ce Annabi (S.A.W) ya aure ta tana budurwa). Sannan ya auri uwar muminai Nana Hafsah ‘yar Umar, sai uwar muminai Nana Zainab ‘yar Khuzaimah, sai uwar muminai Nana Ummu-Salma (asalin sunanta Hindu ‘yar Umaiya). Sannan ya auri uwar muminai Nana Zainab ‘yar Jahsh, sai uwar muminai Nana Juwairiyya ‘yar Haris, sai uwar muminai Nana Ummu- Habiba (asalin sunanta Ramlah ko Hindu ‘yar Abu- sufyan). Sannan sai ya auri uwar muminai Nana Safiyya ‘yar Huyayyi lokacin da akayi yakin Khaibar, sai ya auri uwar muminai Nana Maimunah ‘yar Haris wacce ita ce mace ta qarshe da Annabi (S.A.W) ya aura, Allah ya qara musu yarda baki xayansu.
‘YA’YAN ANNABI (S.A.W).
Dukkanin ‘ya’yayen Annabi (S.A.W) maza da mata in banda Ibrahim, Nana Khadija ce ta haifa masa su. Mahaifiyar Ibrahim ita ce Mariyatul Kibdiyya wacce Mukaukis ya ba da ita kyauta ga Annabi (S..A.W). ‘Ya’yayensa maza sune: Al-kasim (wanda ake yi wa Annabi (S.A.W) alkunya da shi, kuma bai jima ba a duniya ya rasu). Sai xansa Abdullahi shi ne ake masa lakabi da Ad-dahir ko Ad-dayyib domin an haife shi ne a cikin Musulunci. An haifi Ibrahim ne a Madinah, ya rayuW tsawon watanni Ashirin da biyu.
‘Ya’yayensa mata sune: Zainab, ita ce babbarsu, xan goggonta (Abul- Ass) ne ya aure ta. Sai Rukaiyah, mijinta shi ne Sayyadina Usman Xan Affan. Sai Nana Fadimah, mijinta shi ne Sayyadina Ali Xan Abu Xalib, ta haifa masa Al-hasan da Al-husain (shuwagabanin matasan Aljannah).
Sai Ummu-kulsum, Sayyadina Usman Xan Affan ne ya aure ta bayan rasuwar Rukaiyah (Allah ya kara musu yarda baki xayansu).
Imam Nawawi ya ce: “Babu savani kan cewa ‘ya’yayen Annabi (S.A.W) mata su hudu ne, maza kuwa su uku ne a bisa ingantacciyar Magana.”
SIFFOFIN ANNABI (S.A.W).
Annabi (S.A.W) ya kasance mutum ne madaidaici, kuma ya kasance fari ne mai haxe da ja, yana da gashi mai yawa, mai tsananin bakin ido ne. (Allah kasa mugansa Amin suma Amin).
FALALAR ANNABI (S.A.W).
Falalar Annabi (S.A.W) falala ce wanda ba za ta musaltoba ko ta kirgu, amma duk da haka za mu ba da wanda ya kevanta dashi akan sauran Annabawa.
An karbo hadisi daga Jabir Xan Abdullahi (R.A) cewa Annabi (S.A.W) ya ce: “An bani wasu abubuwa guda biyar waxanda ba a ba dasu ga wani Annabi da yazo gabanina.”
An taimake ni da tsorata abokan gaba waxanda tsakanina dasu akwai nisar tafiyar wata guda.
An sanya min qasa ta zamo tsarkakakkiya (wajen yin taimama) kuma gurin sallah, don haka, duk wanda sallah ta riske shi a hanya sai ya tsaya ya yi.
Kuma an halattamin cin ganima wacce bata halttaba ga wani Annabi da ya zo gabanina.
An bani damar yin ceto (a farfajiyar kiyama).
Annabawan da suka zo gabani na sun kasance ana aikosu ne zuwa ga mutanensu kawai, ni kuwa an aiko ni ne zuwa ga mutane baki daya. Bukari da Muslim ne suka ruwaito.
Ya zo a cikin sahihu-Muslim a hadisin Anas (R.A) cewa Annabi (S.A.W) ya ce: “Ni ne farkon wanda zai fara yin ceto ranar qiyama, kuma nafi dukkan Annabawa samun mabiya ranar qiyama, ni ne kuma zan fara qwankwasa kofar Aljanna don a bude.”
Ya zo a hadisin Abu huraira (R.A) cewa Annabi (S.A.W) ya ce: “Ni ne shugaban ‘ya’yan Adamu ranar kiyama, kuma ni ne farkon wanda zai fara fitowa daga kabari ranar kiyama, ni ne kuma farkon wanda zai yi ceto, kuma farkon wanda za’a bashi damar yin ceto.”
MUHIMMAN ABUBUWAN DA SUKA FARU A RAYUWAR (S.A.W).
Isra’I da Mi’iraji (tafiyar da aka yi dashi zuwa masallacin kudus da hawa da akayi dashi zuwa sama), ya faru ne kafin a yi hijira zuwa Madina da shekara uku, a lokacin ne aka farillanta salloli.
SHEKARAR FARKO BAYAN HIJIRA.
Gina masallacinsa, fara kokarin kafa xaular musulunci, farillanta Zakka.
SHEKARA TA BIYU
Yakin Badar babba, (a cikinsa ne Allah ya xaukaka muminai ya kuma dorasu akan abokan gabansu).
SHEKARA TA UKU.
Yakin Uhud, a wannan yakin ne musulmai suka samu rauni saboda savawar da wasu daga cikinsu sukayi wa umarnin Annabi (S.A.W) da shagaltuwa wajen diban ganima.
SHEKARA TA HUDU.
Yakin Banin Nadiir, a wannan yakin ne Annabi (S.A.W) ya fitar da Yahudawan Banin Nadiir daga Madina saboda warware alkawari da sukayi.
SHEKARA TA BIYAR.
Yakin Banil Musdalak, yakin Ahzab, yakin Bani kuraiza.
SHEKARA TA SHIDA.
Sulhun Hudaibiyya, kuma a wannan shekarar ne aka haramta giya har abada.
SHEKARA TA BAKWAI.
Yakin Khaibar, a wannan shekarar ne Annabi (S.A.W) da musulmai suka shiga garin Makka sukayi umara, kuma a shekarar ne ya auri uwar muminai Nana Safiyyah ‘yar Huyayyi.
SHEKARA TA TAKWAS.
Yakin Mu’utata (tsakanin musulmai da Rumawa), fathu Makka, yakin Hunain (tsakanin musulmai da qabilun Hawaz da sakiif).
SHEKARA TA TARA.
Yakin Tabuk, wannan shi ne yaki na qarshe da Annabi (S.A.W) ya yi a rayuwarsa, kuma a wannan shekaran ne mutane suka zo gurin Annabi (S.A.W) suka shiga musulunci qungiya qungiya, shi yasa ake kirar wannan shekarar “shekarar wufudi”.
SHEKARA TA GOMA.
Hajin ban kwana, a shekarar ne Annabi (S.A.W) ya yi hajji tare da musulmai sama da dubu xari.
SHEKARA TA SHA ‘DAYA.
A farkon wannan shekarar ne Annabi (S.A.W) ya yi wafati, ya yi wafati ne ranar Litinin cikin watan Rabi’ul- Awwal duk da cewa anyi savani wajen kididdige kwanan watan. Annabi (S.A.W) ya yi wafati ne yana da shekara sittin da uku (63) a rayuwarsa, Arba’in (40) daga ciki kafin a aiko shi, ashirin da uku (23) kuwa yana Annabi kuma Manzo, shekara goma sha uku (13) daga ciki ya yi sune a Makka, sauran goman (10) kuma a Madinah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da Alayensa da sahabbansa).
AMMOMIN ANNABU (S.A.W).
Al-haris, Zubair, Abu Xalib, Hamza, Al-Gaidak, Dirar, Al-mukawwam, Abu Lahab, Abbas, Amima, Ummu Hakima, Barra, Atika, Safiyya da kuma Arwa.
MAI TSARON K’OFAR ANNABI (S.A.W).
Anas Xan Malik.
MAWAKAN ANNABI (S.A.W).
Hassan Xan Sabit, Abdullahi Xan Rawahata, Ka’abu Xan Malik.
LADANAN ANNABI (S.A.W).
Bilal Al-Habashi, Abdullahi xan Ummu Maktum, Sa’ad Al-kirdi.
TAMBARIN ZOBEN ANNABI (S.A.W).
(Muhammadur Rasulullah).

Ya ‘yan’uwa musulmai! Ku duba irin wannan rayuwa ta Annabinmu (S.A.W)! Shin haka rayuwarmu take? Ko dai bamu sakankance bane cewa wannan Annabi shi ne Annabin da aka aiko mana? Ku tuna da fadin Allah Maxaukakin Sarki da yake cewa: “Haqiqa kuna da abin koyi mai kyau game da Manzon Allah.” Suratul Ahzab, Aya ta 21.

Allah ya bamu ikon koyi dashi, Amin.
Ina yiwa dukkan ‘yan uwana maza da mata murna da zagayowar ranar haihuwar Shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W), Allah shi maimaita mana ya bamu zaman lafiya a Najeriya.

Daga xan uwanku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here