WANENE MUKTAR ADNAN?

0

WANENE MUKTAR ADNAN?

Alhaji Muktar Adnan ya zama Hakimim danbatta kuma Sarkin Ban Kano a shekarar 1954, wadda kuma ta yi daidai da shekarar da aka zabe shi a zaman dan Majalisar Wakilai ta Tarayya ta farko da ke Ikko, yana wakiltarta gundumomin kiru da karaye a lokacin da Turawa ke mulkin kasar nan, har kuma zuwa jamhuriya ta farko, wadda aka yi tsakanin shekarun 1960 zuwa 1966.

dan takaitaccen tarihin wannan dan taliki Basarake kuma dan siyasa, ya nuna yana daga cikin Hakimai hudu (Madaki da Sarkin Bai da Makama da Sarkin Dawaki mai Tuta) masu zaben Sarkin Kano, wanda kuma a yau shi kadai yake raye daga cikin wadanda suka zabi Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayaro, a matsayin Sarki a shekarar 1963.

Kazalika yana daga cikin `yan siyasar farko na kasar nan da suka shige gaba wajen samo wa kasar `yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. A bana yana da shekaru 94, a duniya.

Shi ne Hakimin da ya fi kowane Hakimi a nan Arewa tsawon kwana kan karagar mulki, inda ya shekara 60, wadda a Kudanci da Gabashin kasar nan ma, ina jin sai an tona.

An haifi Alhaji Muktar Adnan a unguwar kofar Gabas ta garin danbatta a shekarar 1926, kuma kamar yadda yake a al`adar Hausawa musulmi, tun yana dan shekaru 4 da haihuwa ya shiga makarantar allo, don samun karatun Alkur`ani mai tsaki. A lokacin da ya kai shekara 9, aka sa shi makarantar Elmentare ta danbatta, tsakanin shekarun 1935 zuwa 1939.

A tsakanin shekarun 1939 zuwa 1944, ya zarce zuwa makarantar Midil ta Kano ta wancan lokacin da a yau ake kira Kwalejin Rumfa, makarantar da ta zama daya tilo a lokaci mai tsawo, inda duk wani dan asalin tsohon lardin Kano, (lardi da a yau ya kunshi jihohin Kano da Jigawa), a nan ya yi karatunsa na boko.

Bayan kammala makarantar Midil ta Kano, bisa umurnin mahaifinsa, wanda yake Hakimin Danbatta kuma Sarkin Ban Kano, ya koma garin danbatta, inda ya fara aiki a zaman magatakarda ga mahaifinsa. Bayan ya yi shekara daya, a zaman Malamin Hakimi, sai aka tura shi Kwalejin Horar da Akawuna da ke Zariya, inda ya nuna matukar kwazo, don haka maimakon ya koma bakin aikinsa na danbatta, ko En`en Kano ta waccan lokacin, sai aka wuce da shi Kaduna a cikin aikin gwamnatin Arewa, inda aka ba shi mukamin mai binciken kudi (odita). A kan wannan mukami ne ya yi aiki a garuruwan Zariya da Kano. Daga bisani kuma sai ya dawo da aiki a En`en Kano, a matsayin mataimakin Akanta.

Shigowar harkokin siyasa da Turawan mulkin mallaka suka bullo da ita a zaman shirye-shiryen ba da mulkin kai, a shekarar 1954, an zabi Alhaji Muktar Adnan a matsayin dan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar kiru da karaye, Majalisar da ya zauna har karo biyu, ko in ce har zuwa lokacin da sojoji suka yi juyin mulkin farko na ranar 15 ga watan Janairun 1966, wanda yin wancan juyin mulki ya kawo karshen harkokin siyasar jamhuriyar farko, hakan kuma ya sanya mai girma Sarkin Ban Kano ya dawo kan kujerarsa ta Hakimin danbatta, sarautar da da ma yake rike da ita a dai shekarar da ya tafi Majalisar Wakilan.

A tsawon shekaru 12 da mai girma Sarkin Ban Kano ya yi a Majalisar Wakilai ta Tarayya, shi ne Babban Mai Tsawatarwa a Majalisar, mukamin da ya dana a cikin yana da karancin shekaru, sannan da ilmin boko, abubuwan da suka ba shi damar kasancewarsa tamfar wata a daren 15, a Majalisar, ta yadda idan za a yi wani kuduri mai nauyi, irin su Sarkin Bai akan sa gaba su gabatar.

Alal misali, a shekarar 1962, da madugun adawa na wancan lokacin Cif Obafemi Awolowo, ya je London ya bayar da wata lacca, wadda a cikinta ya soki gwamnatin tarayya a kan tana da rauni don haka ba ta dace da a ce ita ke gudanar da mulki ba, Alhaji Muktar Adnan aka sanya ya gabatar da wani kuduri da ya zama martani da kuma yin tir da Allah-wadai da abin da Cif Awolowo ya yi a kasar ta Birtaniya, wadda suka kalla zubar da mutuncin kasa a idanun duniya. Duk da yake `yan adawa sun yi kokarin su hana samun nasarar wancan kuduri, daga karshe sai da kudurin ya kai labari, Majalisa dai ta yi tir da Allah-wadai da abin da Madugun adawa Cif Awolowo ya yi a London.

Yau kwatsam sai naci karo da labarin da ke cewa Sarkin Bichi Aminu Ado ya tsige shi daga matsayin Hakimi.

Allah ya kyauta
Daga shafin taskira H online

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here