DAKARUN DAJI SUN KOMA FASHI DA MAKAMI.
Daga Taskar Labarai
A ranar litanin 09-12-2019 da misalin 10:00am dakarun daji dauke da miyagun makamai suka tare masu dakon shinkafa a daidai cikin garin Ruma Sabon gari, lokacin da suke loda shinkafar a babura kwatsam sai ga motar jami’an tsaro, take dakarun dajin suka basu hannu cewa su wuce haka suka gyalala suka wuce abinsu. Dawowarsu ke da wuya bayan ‘yan bindigar sun gama wasashen shinkafar sun tafi.
Sai mutanen gari suka kama yiwa jami’an tsaronan eho eho, wannan yasa suka garzaya wajen Galadiman Ruma domin kai kokensu, hakan yasa ya tsawata wa mutanen gari kan matakinsu akan jami’an tsaro.
Haka kuma duk dai a ranar litanin din, ‘yan banga sun koro wasu shanu kimanin talatin daga wajan Karare da a ke zaton sato su aka yi daga wani waje mai nisa, sun iso daidai Tadeta gab shiga Batsari sai ga Dakarun daji kan babura kowane babur yana dauke da mutum ukku a guje, suka kebe shanun nan suka kuma zaro adduna suka cewa ‘yan bangar nan baku isa ku tafi da shanun nan ba.
Hatsaniya na neman kabrewa aka kira jami’an tsaro suka lallashi fulanin nan aka isa da shanu sakatariyar karamar hukumar Batsari daga bisani dai aka basu shanun sukayi gaba dasu ba tare da sanin hakikanin halattaccen mai su ba.
A ranar talata 10-12-019 ma da rana tsaka dakarun na daji sun tare hanyar Kandawa zuwa Kurmiyal inda suka yi wa mutane kwacen wayoyi da kudi masu dakon shinkafa kuma aka karbe, haka nan ma hanyar Jibiya zuwa Batsari sun tare dai dai Kabobi da Garin Inu inda nan ma suka yi wa mutane kwacen wayoyi da kudi, su kuma masu dakon shinkafa an yita karkatar da su zuwa daji inda dabarsu take domin kai masu ita can sannan a sallamesu su gane garinsu.
Haka batun yake a ranar laraba 11-12-019, sun tare hanyoyi inda suka kora wani mai dakon shinkafa shake da shinkafar cikin mota kirar gwab, bayan ya kai masu ita inda suke so suka sallameshi wannan ya faru ne a kan hanyar Kandawa zuwa Kurmiyal wanda daga bisani jami’an tsaro mota ukku suka shiga lungun sukayi ‘yan harbe harbensu suka fito ‘yan bindigar kuma dai sun sha ba tare da ko kwarzane ba.
A ranar alhamis 12-12-019 da misalin 11:00 na dare dakarun na daji sun kai hari a kauyen Gajen-Tsamiya da Gajen-Tsauni inda suka yi harbe-harbensu suka yi garkuwa da wani Mal. Hamza sannan suka yi gaba da shanun noma guda biyu.
A cikin makon da ya gabata ma sunyi garkuya da mutane hudu a kauyukan Shirgi da Karare kuma sun kashe wani mutum Mallam Umaru na gwandu a kauyen Yandaka duk a cikin yankin karamar hukumar Batsari.
Sannan a ranar juma’a 13-12-019 ma dakarun dajin sun tare hanyoyin da suka saba tarewa inda suka rika amsar N300 ga duk dan babur mai dakon shinkafa, N3000 ga ‘yan gwab din da ke dauke da shinkafa, amma sun karbe ma wani dan gwab buhun shinkafa biyu a daidai Dankar saboda sun raina kudin da ya basu.