KASO 70% NA KUƊAƊAN DA AKE TAFIYAR DA RESTORATION VANGARD SUNA TAFIYA NE ALJIHUN MA’AIKATAN GWAMNATI.

0

KASO 70% NA KUƊAƊAN DA AKE TAFIYAR DA RESTORATION VANGARD SUNA TAFIYA NE ALJIHUN MA’AIKATAN GWAMNATI.

~~~~ Inji mai ba Gwaman Shawara..

A jiya ne wajen kare kasafin kudin shekara ta 2020. a gaban zauran da ake kare kasafin kuɗi na majalisar dokokin jihar Katsina, A ƙalkashin jagorancin shugaban kwamitin kare kasafin kuɗin Rt Hon, Aliyu Sabiu Muduru Walin Gabas Cigarin Mani.

Mai ba gwamna shawara a kan harkokin matasa ya yi karin bayani gani da fashin baki. Akan zunzurutun kuɗin da yawansu kai Naira million 60 zuwa 70, wanda ake warewa domin tafiyar da kungiyar Restoration Vanguard.

Wannan Kungiya dai a da mai girma gwamna shi ne yake ɗaukar nauyinta da aljihunsa kafin a faɗaɗata zuwa kananun hukumomi, daga baya aka maido akalarta a cikin ma’aikatar jin daɗin matasa.

Da kwamitin kare kasafin kuɗi yake tambayarshi dangane da kuɗin da ake cirwa duk wata, sai yace ana ciresu ne duk wata amma dai baisan yadda ake yi da suba.

ya bayyana cewa ya bayar da shawara irin hanyar da ta dace domin kaucewa abin da zai taso, yace ya kamata ayi tsari wajen rabon kuɗin sa’an nan a san adadin mutanan da suke amfana da kuɗin, ta hanyar bude wa kowannan su asusun ajiya na banki.

Yaci gaba da cewa da yawa daga masu amfana da kuɗin yasan akwai ma’aikatan gwamnati. Sai kaga mutum yana aijin gwamnati kuma ya a cikin kungiyar yana amsar kudin kungiyar.

Yace ya kamata ayi tsari domin ganin an yi abin da zai amfani matasa da suke amfana da shirin, Inda daga nan kwamitin kare kasafin Kuɗin ya sanya alamar tambaya a kan kudin inda ya nemi aka wo masu yawan adadin mutanan da suke amfana da shirin.

Daga karshe da aka tambayi mai ba gwamna shawara a kan makomar kungiya? sai yace yana ganin cewa kamar gwamnati zata dauki wasu daga cikinsu domin mayar dasu ma’akatar sabuwar hukumar nan ta KASAROTA.

Daga
Abdurashid Musa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here