Kungiyar Fityanul Islam Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Mai Martaba Sarkin Kano

0

Kungiyar Fityanul Islam Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Mai Martaba Sarkin Kano

Daga Rayyahi Sani Khalifa

Shugaban Kungiyar Fityanul Islam ta kasa, Sheikh Muhammadu Arabi Abulfathi ya bayyana goyon bayan Kungiyar Fityanul Islam ga Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi ||.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata ziyara da ya kaiwa Sarkin a fadarsa, shugaban ya tabbatarwa Sarki cewa dukkan ‘yan Fityanul Islam na kowace jiha da kananan hukomomi a fadin Najeriya suna tare da shi kuma suna mishi adduo’in samun nasara akan makiyansa, suna tare da shi kamar yanda maulanmu Shehu Dahiru Usman Bauchi RTA yake tare da shi. Shugaban yayi kira ga sauran ilahirin ‘yan tijjaniyya kama daga Shehunnai da muridai da su bi sahun maulanmu Shehu Dahiru wajen marawa Sarki baya.

A nasa jawabin mai martaba yayi maraba da ziyarar da kungiyar ta kawo masa, kuma ya bayyana godiyansa ga irin goyon bayan da yake samu wajen ‘yan uwansa tijanawa, ya kuma bayyana cewa kakaninsa da babansa ‘yan tijjaniya ne kuma shima dan tijjaniyya ne, kuma yana yin tijjaniyya ne ba dan ya gada wajen iyayensa kawai ba, a’a se dan amfaninta da yake gani.

See also  THE BUHARI ADMINISTRATION TRAINS 4,572 KANO RESIDENTS ON POULTRY FARMING!

Kungiyar Fityanu ita ce Kungiya mafi girma da shahara a kungiyoyin darikar tijjaniyya, domin itace Kungiya daya tilo a tijjaniyya da take da shuwagabbani da mambobi a kusan kowace jiha da kananan hukumomi a fadin Najeriya, sannan itace Kungiyar da ke wakiltar ‘yan tijjaniyya a gwamnatance a kusan dukkan jihojin Najeriya. It a keda Kungiyar agaji ta darika masu fararen uniform wanda kusan kowa ya sansu a Najeriya saboda yawansu a birane da kauyuka da kuma irin ayyukan bada tsaro da suke aiwatarwa a masallatan jummu’a da wuraren taron darika da musulunci baki daya.

Allah ya daura sarki akan makiyansa bijahi sayidul wara amin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here