SU WAYE RESTORATION VANGUARD A KATSINA

0

SU WAYE RESTORATION VANGUARD A KATSINA?

Daga Taskar labarai

Kwanan nan wani rahoto ya fasu a yanar gizo, inda aka ruwaito cewa mai ba gwamnan Katsina shawara a kan harkar matasa Alhaji Ibrahim Khalil ya fada a zauren majalisar jihar Katsina cewa, ana kashe sama da naira miliyan sittin duk wata ga wasu matasa a jihar da ake ce ma Restoration Vanguard.

An ruwaito cewa, mai ba gwamnan shawara ya fadi zancen a gaban ‘yan majalisar da yaje kare kasafin kudin hukumar sa na 2020. Kwamitin kasafin kudin da dan majalisa Alhaji Aliyu Sabi’u Maduru ke jagoranta.

Kodayake marubucin labarin ya sake, fitar da wata sanarwar yace, sam bai fahimci bayanin daidai ba, a tattaunawar da aka yi da majalisar ba maganar kudin basu kai adadin da ya bada a rahoton shi ba.

Taskar labarai sun yi zurfafan binciken su waye wadannan matasa masu suna Restoration vanguard? Su waye shugabannin su? Nawa ake kashe masu? Su nawa ne? Meye ra’ayin jama’a akan su?

Binciken mu ya gano matasan nan sun kai mutane dubu biyar da dari daya da Goma uku 5113. daya a duk fadin jihar Katsina.
Shugaban su kuma shine Alhaji Muntari Lawal babban mai baiwa gwamnan Katsina shawara kuma shugaban ma’aikatan gidan gwamnati. Kwamandan su shi ne Alhaji Wada Abubakar ( Wanda aka fi sani da wada forotokol)darakta janar na Masaukin bakin gwamnan Katsina.

Sai shugaban ciyamomin shiyya-shiyya Samaila Malam Dabo Kofar Durbi. Sakatare Abdullahi Isah Bage Tudun Wada. Sai sauran ciyamomin kananan hukumomi da kuma na shiyya-shiyya. Umurni na fitowa ne daga sama zuwa kasa.

Taska ta gano kungiyar na aiki kafada da kafada da jami’an tsaron ‘yan sanda don samun nasarar gudanarwarsu. Don haka, hukumomin tsaro sun san da zamansu.

An kafa kungiyar a 2016 da mutane Goma amma a 2017 aka yi mata tsari ingantacce. Da tsarin alawus na wata-watada kuma aikin da zasu rika tafiyarwa.

An tsara aikinta. Hana cin zarafin masu rike da mukamai a wajen taro, hana bara da maula ga masu rike da mukamai a wajen taro, hana tashin hankali a wajen taro, hana daba da dawo da hankalin matasa a kan shan kwaya ayi banga a taro.

Taska ta gano cewa duk wadanda ake dauka a ciki, matasa ne da suka taimaka wa jam’iyyar APC suka kai ga gaci. Mai makon a kyale su sakaka sai aka tara su a karkashin inuwar kungiyar.

Sai kuma matasa na garuruwa da unguwanni da aka san tantirai ne, sai a jawo su a saka su, don su natsu.

Kowane gari ko karamar hukuma, ana sa babba mai mukami a gwamnatin ya kawo wadanda yake ganin sun cancanta su zama cikin kungiyar. Da haka aka tattara membobin kungiyar na jahar baki daya.

Duk memba yana da Riga da katin shaida an kuma da lambar wayarshi da adireshinsa.wanda ana iya bukatar sa kowane lokaci.

Taska ta gano ana biyan membobin alawus kashi biyu, akwai wadanda aikinsu na koyaushe ne suna amsar naira dubu ashirin. Sai kuma sauran suna amsar naira dubu Goma-goma.

Tun da ake ba a taba fashin biyansu ba.Taska ta gano, daga wasu takardun fitar da kudin da ta gani na kudin da ake biyansu. kudin sam ko kusa da miliyan sittin ko Saba’in basu kai ba.

Takardun sun bambanta wasu miliyan ashirin da tara wasu kuma talatin da doriya. Koda yake kudin na karuwa saboda sabbin membobin da ake dauka.

Taska ta gano ana fitar da kudin a bisa tsari kuma ma’aikatan gwamnatin Katsina ke biyan kudin a bisa tsarin biya akan tebur.

Taska ta gano wasu daga matasan nan sun natsu saboda wadannan kudaden da suke amsa duk wata, kuma ta gano wasu hatsabiban yaran da suka hankalta saboda shiga tsarin kungiyar.

Shugabannin kungiyar Samaila Malam Dabo da kuma Abdullahi Isah Bage sun ce aikin su ya taimaka wajen hana bangar siyasa da barna da tada hankali a siyasar da ta gabata ta 2019 yace mun yi ma kanmu tsarin da duk wani takadari mun sa yayi shiru. Inji su da suna magana da Taskar labarai.

Suka ce mun kuma yi nasarar hana a ci ma shugabannin mu mutunci a taro, yace in zaka iya tuna abin da wasu ‘yan iska suka taba yi wa mai girma gwamna a hawan sallar farko da aka yi. Inda mai girma gwamna ya sauko daga kan bene don gaisuwa da sarki, inda wasu ‘yan iska suka tada kura da kyar jami’an tsaro suka shawo kan lamarin, kaga irin wannan ya sake faruwa? Inji samaila Malam Dabo Kofar Durbi.

Sun kara da cewa, taimakon matasan nan kamar wani jihadi ne, wanda gwamnatin nan tayi, kuma ana ganin amfaninshi a aikace.
Taska ta gano wasu kwamishinoni da masu bada shawara da suka San aikin matasan kungiyar suna fatan a maido kulawarsu karkashinsu.

Malam dabo yace a lokacin PDP an yi irin wannan wanda ana kiran kudin da kudin ‘yan iska,kuma aka rika abin ba tsari,a lokacin dubu biyar ake bayarwa sama da shekaru goma da suka wuce, kuma matasan aka rika basu kwaya da kuma ingiza su ga daba da tashin hankali.

Amma a tsarin mu ta Restoration Vanguard babu shan kwaya babu kauranci ba daba kuma ina kalubalantarka kaje ka bincika dan kungiyar da aka taba kamawa da daya daga cikin abin da na shaida maka inji sakatare da shugaban kungiyar.
Amma ‘yan PDP da muka zan ta dasu,ba haka suke kallon yan kungiyar ba, su suna masu kallon wasu sojan sa kai ne da aka yi amfani da su a zaben da ya wuce kuma za a iya amfani da su a nan gaba.

Zargin da shugabannin kungiyar suka musanta na Cesar basu da Sana’a kuma basu karatu sun bayyana cewa, “Muna da tarbiyya da tsari, da yawan membobin suna karatu da sana’a da taimakon abin da kungiyar ke bamu.”
._______………___________________________________
Taskar Labarai da The Links News Jaridu ne masu zaman kan su dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com kuma suna bisa duk shafukan sada zumunta na Facebook, Twitter, YouTube da sauran su .07043777779.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here