ZAZZAƁIN RANA NA DISAMBA 26, 2019

0

ZAZZAƁIN RANA NA DISAMBA 26, 2019

Salaamun alaikum.

Shi wannan Kusufin na Rana, wanda tun kusan wata muka sanar zai faru a disamba ɗin nan, kuma a can baya ma mun ɗanyi tsokacin zai faru, inda muka ce za a yi zafafan Kusufai guda shida ne a tsakanin na Wata da na Rana a shekara ta 2019, muka ce uku za su shafi Afirika, ukun kuma za su shafi Gabas ta Tsakiya ne da wasu Ƙasashen – waɗanda su suna nuni ne akan rugujewar Az-zaluman Shugabannin Gabas ta tsakiyane da wasu ƙasashen, to wannan yana daga cikin wanda Najeriya ba zata ganshi ba, ga ƙasashen da za su gani nan:

Sa’udiyya, Ƙaɗar, United Arab Emirates, Oman, India, Sri Lanka, Malaysia, Indonesia, Singapore, Northern Mariana Islands, and Guam.

Hakanan zai haɗa da waɗannan guraren:

Kozhikode, Coimbatore, Jaffna, Trincomalee, Sibolga, Tanjung Pinang, Batam, Singapore, Singkawang and Guam.

Garuruwa kamar su Doha, Madurai, Pekanbaru, Dumai, Johor Bahru and Kuching ba za su shaida Kusufin ba.

Muhimmin mu idan Allah yasa ya faru to Masana suna tabbatar da cewa alama ce ta rugujewar Sa’udiyya da Az-zalumansu da Zaluncinsu gaba ɗaya daga samuwa a duniya, akai yiwuwar mace-mace na Manya a ƙasashen, wanda muke fatan harda Shugaban Sa’udiyya ko da Yarimansa ko gaba ɗayansu (Shugabannin Fasiƙanci da Fajirci) – Wallaahul-aalim, “Yamhullahu maa ya shaa’u wa yuthbit”.

Duk wannan sanarwa ne da zuwan Imamul-Hujjah (A), wanda shine zai kawar da dukkanin Rashin adalci da Wulaƙanci da Ƙasƙanci da Az-zalumai da Zalunci na duniya baki ɗaya.

Wajibi ne mu tanadi ayyukan sauraron bayyanar Imamul-Mahdiy (A) don mu zamo daga “Ansaar” ɗinsa (A)! Mu yawaita kyawawan ayyuka, mu guji munanan ayyuka, mu ringa Sallar dare! da sauran abubuwa na taren zuwan Imamul-Mahdiy (A).

Allah ka gaggauta fitowar Imamunaz-zamaan (A) na sarari, Allah ka baiwa Sayyid Zakzakiy da matarsa da sauran Muminai lafiya, ka kuɓutar da su daga hannun Az-zalumai, albarkacin Manzo da Alayensa alaihimus-salam.

Daga Hadiminku Sayyid Nuru Daruth-thaƙalaini

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here