SARKIN KANO DA SARAKUNAN GANDUJE

0

SARKIN KANO DA SARAKUNAN GANDUJE

Daga taskar labarai

A yau mai martaba sarkin Musulmi yaje birnin Kano domin halartar bikin murnar cikar asibitin kashi shekaru sittin da ginawa.

A shekaru sittin da suka gabata Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I shi ne Wanda ya bude shi. Sarkin musulmi na gab da shigowa Kano, sai sauran sarakuna hudu wadanda lamarinsu ke a gaban kotu suka fara shirin zuwa filin jirgi don tarba.

Sai sarkin musulmi ya aika da cewa wanda ya amince ya tare shi shi ne sarkin Kano na gaskiya Alhaji Muhammadu Sanusi II, wannan lamari ya bata ran sauran sarakunan.

Kuma irin wannan ke fusata gwamnatin Kano aji tayi tsuwwa, yanzu in ba ayi hankali ba kafin safiyar gobe sai kaji sanarwa daga fadar gwamnati.

A baya duk lokacin taro a fadar shugaban kasa, ko kuma taro sarakunan kasar nan. Sai kaji a takardar gayyatar ance sarkin Kano Muhammadu Sanusi II aka amince ya halarta da an yi haka sai kaga gwamnatin Kano ta shaqa.

Akwai taron da wani sarkin cikin sarakunan Ganduje yana gab da yayi karambanin shiga taro yaga me zai faru aka bashi shawarar kar ya fara don kuwa zai jawo wa kansa abin kunyar ‘ya’ya da jikoki sai kawai ya koma yayi likimo a masaukinshi.

A wurin fadar shugaban kasa da majalisar sarkaunan kasar nan , sarakuna kala biyu ke a Kano. Sarkin Kano da sarakunan Ganduje.

Gwamnatin Kano tayi-tayi su amsu, amma kamar ana tallar turmi a tsakiyar Legas, duk ko ina cewa ake zancen yana kotu.

Don haka gwamnatin ke ta takurawa, sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, don dole ya amince da sarakunan Ganduje don duniya ta yarda dasu, wannan dambarwa ita ake ciki a yanzu.
_______________________________________________
Jaridar Taskar Labarai jarida ce mai zaman kanta da ‘yar uwarta ta Turanci The links News suna a bisa www.taskarlabarai.com da www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta da WhatsApp na 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here