LAMBAR WAYA TA HADDASA KISAN KAI A BATSARI.

0

LAMBAR WAYA TA HADDASA KISAN KAI A BATSARI.

Daga Taskar Labarai

A ranar litanin 23/12/2019, wani abin ban takaici ya faru a wani kauye mai suna Kasai dake cikin yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina.

Inda wani mutum Mallam Badamasi da ‘ya’yansa guda biyu suka kashe wani direban mota mai suna Salihu dukkansu mazauna garin na Kasai.

Mallam Badamasi yana bincika wayar matarsa wacce ya aure ta tana bazawara, sai yaga lambar Salihu, nan take sai ya dauki wayarshi ya kirashi ya sanar da shi cewa yazo gidansa yana son ganinsa, sai shi Salihu ya bayyana masa cewa yana Batsari yana gyaran mota amma idan ya kammala ya dawo gida zai zo.

Da ya gama ya koma gida Kasai sai ya ajiye motarsa a kofar gidansa yace wa yaron motar ya jirashi zai je gidan Mallam Badamasi domin ya kirashi ta waya yace yana son ganinsa bai san dalilin kiran ba, yaron mota yayi ta jira har dare yayi bai ga ya dawo ba sai ya shiga motar ya kulle yayi kwanciyarsa.

Amma da isar Salihu gidan Mallam Badamasi kawai suka kewashi da duka da itace , suka yi masa jinjina sannan suka daureshi har gari ya waye, sai shi Mallam Badamasi yaje gidan mai unguwa ya sanar dashi aika-aikan da suka yi wannan mutum take aka sanar wa jami’an tsaro suka zo domin bincike shi kuma aka garzaya dashi asibiti amma dai daga bisani rai yayi halinsa.

Wannan labari yana karade karkara sai ga dakarun daji dauke da miyagun makamai sun dumfaro garin akan babura sama da talatin sun shigo ta wani kauyen Nahuta zasu wuce Kasai suna cewa yau sai sun tada garin, amma sai aka gaya masu cewa antura jami’an tsaro domin daukar matakin da ya dace, daga nan sai suka dakata suka ce zasu jira suji abinda hukuma zata yi.

Da yake shi Salihu direba an sanshi sosai a duk Karkarar yana da kamun kai da hakuri wajan gudanar da sana’rsa, yakan dauki jama’ar Fulani idan bukukuwansu ya tashi ya kaisu ba tare da raina duk abinda zai samu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here