WADANNAN SHIRGA SHIRGAN MATAYE MARUBUTAN, SHIN DA A CE MAZAJE NE WAI MATAYE NAWA KOWACE ZATA AURA NE?

0

WADANNAN SHIRGA SHIRGAN MATAYE MARUBUTAN, SHIN DA A CE MAZAJE NE WAI MATAYE NAWA KOWACE ZATA AURA NE?
Daga Bala Anas Babintala
1. Balaraba Ramat Yakub
2. Rahma Abdulmajid
3. Bilkisu Yusuf Ali
4. Fauziyya D. Sulaiman
5. Maimuna Idris Beli
6. Amina Hassan Abdussalam
Tarihin rubutun kirkirarrun labaran Hausa ba zai taba cika ba tare da an sanya sunayen wadannan mashahuran matayen ba. Ba wai na zabe su ba ne don su kadai ne shahararru, na zabe su ne don kasancewarsu masu Akida iri daya. Wato Akidar Namiji na tauye Hakkin mata.
Abin tambaya a nan shi ne, wai wadannan matan shida, da mazaje ne yaya dabi’arsu zata kasance tsakaninsu da matayensu? A matsayina na marubuci namiji na dora su daya bayan daya a mizani, na yi nazarinsu a matsayin mazaje.
Zan dauke su daki daki na yi sharhi dangane da fahimtar dana yi musu.
1. Hajiya Balaraba Ramat, dadaddiyar marubuciya wadda littattafan ta mafi rinjaye suke zargin maza da rashin yin adalci ga mata, mace ce mai raha da saurin sabo da mutane. Hakika Hajiya da namiji ce ‘yar kasuwa ce. Bana raba daya biyu da Namiji ce mata hudu zata yi.
Hujja: Mace ce mai kasaita. Saboda haka dole ta auri mata hudu don ta kece raini. In da a lokacin bayi ne ma to har da Kwarkwarori.
2. Rahma Abdulmajid, Sayyada ta fara rubutu tun da karancin shekaru, ko da yake ba duk rubutunta ke nuna zargi ga maza suna tauye mata ba, amma ba boyayyen abu ba ne ga duk wanda ya santa a zahiri bata boye ra’ayinta ga yadda maza ke tauye mata. Tana da raha kuma bata bakunta a duk in da ta samu kanta. Muhawara da ita bata da dadi saboda mayyar kafa hujjoji ce. Kasancewarta malamar Addini kuma Hadima, Mukaddima, in da Namiji ce ko shakka bana yi mata hudu zata aure, kuma ba zata bar su a gari daya ba. Zata rarraba su ne, mai yiwuwa ta bar daya a Lagos, daya a Abuja, daya a Kaduna, dayar kuma a Kano.
3. Bilkisu Yusuf Ali, Nana Bilkisu, mai cin tudu biyu kenan, Addini da boko. A rubutunta da lafazanta bata taba boye Namiji ba dan goyo ba ne. Gata dai ‘yar boko ce, amma malantar addini da hidima ta rinjayi bokon a dabi’ar ta. Wanda hakan ya sanya in da namiji ce ko tantama bana yi mata uku zuwa hudu zata aura saboda kasaitar malanta.
4. Fauziyya D Sulaiman, magen Lami kenan, ba cizo ba yakushi. Mace ce mai kazar kazar, bata san lalaci ba. Ko da yake yawancin mutane zasu yarda da ni cewa bata dauki duniya da zafi ba, amma ta shigo cikin wannan rukunin ne saboda tunani iri daya da na sauran ‘yan uwanta cewa maza na tauye mata. Hausawa sun ce da ganin kura zata ci akuya, mutum na kallon ta ya san in da Namiji ce bata yi kama da masu zama da mace daya ba. Tabbas in da Namiji ce mata biyu zata yi. Hujja: ba safai mutum mai kazar kazar ke iya zama da mace daya ba.
5. Maimuna Idris Beli, Dila Sarkin wayo, a duk cikin rukunin matan nan babu mai wayonta, duk da kasancewar ta ‘yar karamar ko kuma na ce mai ‘yar tsabar cikinsu. Ita ma ta yarda lallai Namiji ba dan goyo ba ne, duk da cewa da namiji ce dole mata uku zata aura. Hujja: don ta raba kawunan su kada su hade mata kai.
6. Amina Hassan Abdussalam, ita ce mafi karancin maganar cikinsu, haka nan baturiyar cikinsu. Zai yi wuya mutum ya gane cikakken ra’ayinta game da rashin kirkin maza, saboda rashin yawan maganarta. Amma dai ita ma ta yarda Namiji ba dan goyo ba ne. Sabanin sauran matan da na yi bayani a kansu, Amina cikakkiyar Nasara ce, babu shakka in da Namiji ce zai yi wuya ta auri mace fiye da daya.
Wannan shi ne ra’ayina game da wadannan matayen marubuta, abin tambayar a nan shi ne, wai wadannan matan in da mazaje ne zasu iya yiwa mata adalci kamar yadda suke bolokokon nemawa mata ‘yancin kuwa, ko dai su ma sajewa zasu yi kawai ruwa ta sha. Sau tari nakan yi tunanin yakin su da maza yafi kama da siyasa maimakon neman ‘yanci.
Bala Anaas shahararren marubucin hausa ne da kuma shirya fina finai. Yana cikin jigo Adabin kasuwar Kano da kuma kannywood

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here