YADDA MUKA AZABTU A FILIN JIRGIN ABUJA

0

YADDA MUKA AZABTU A FILIN JIRGIN ABUJA

Daga Ahmad Muhammad

@Taskar Labarai

Na baro Legas nazo Abuja a ranar kirsimati ranar 26 Disamba na yi niyyar zuwa Kano, na sayi tikitin kamfanin jiragen Max in da aka tsara tashin mu karfe shidda na yamma.

Karfe biyar aka kawo ni filin jirgi, duk muka iske wadanda suka sayi tikitin sun iso filin jirgin a cike jirage na sauka da tashi.

Ban an kara ba, sai na ga har tara na dare tayi ba a kira mu ba, na tambaya jirgin mu yana nan? Aka ce mani Maxair Vm 1601 yana nan tsaye tun da ya dawo daga wata tafiyar.

Na nufi ATM in samu Karin kudi, sai katin ya makale, wohoho saura yan canji aljifuna na rasa abin dake mani dadi a duniya.
nayi ta kiran lambobin dana sani matsalar samun layi ya sa ba nasara wasu kuma wayoyin a kashe.

Ga yunwa ga damuwa ga ba wani bayani, wasa-wasa har karfe daya na dare, tun karfe shidda na yamma.

Daga baya na samu labarin cewa jirgin ya kasa tashi ne, don yanayin sararin samaniyar Kano baya da kyau ga sauka ko tashin jiragen sama.

See also  Taron PDP ne ya firgita APC ta tsayar da buhari takara- Sule Lamido

Wani abu sai kasata Najeriya, inda ace inda aka ci gaba ne, za a bamu hakuri, a bamu abinci, a kuma samar mana motar da zata kai mu masauki.

Amma a ranar naga wadanda kuru kawai su ka yi suka zo hawan jirgin don saboda da titin daga Abuja zuwa Kano ya zama mafi hatsari a arewacin kasar nan,don haka a filin suka kwanta kamar yan gudun hijira.

Ni da azaba ta isheni wani Dan taksi na sa ya dauko ni zuwa gidan wani abokina, na soke zuwa Kano ban san ya sauran suka kare ba.

kun ji labarina Taskar Labarai.

Ahmad dan kasuwa ne mazaunin Kaduna ya rubuto mana wannan, ana iya samunsa a email ahmad123@gmail.com

NB. Taskar labarai tayi bincike akan ikirarinsa kafin ta buga labarin nasa, tabbas a jiya an samu matsalar yanayi a Kano kuma lallai jirage sun yi wahalar tashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here