AKWAI GIBI BABBA TSAKANIN DABARUN YAKIN BOKO HARAM DA NA DAKARUN TSARON NIGERIA

0

AKWAI GIBI BABBA TSAKANIN DABARUN YAKIN BOKO HARAM DA NA DAKARUN TSARON NIGERIA

Daga datti Assalafiy

Ina fata wannan sakon nawa zai riski Masoyina Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya

Yau sati bakwai da suka gabata, wato ranar juma’a 8-11-2019 shugabannin kungiyar Boko Haram/ISWAP suka nada sabbin kwamandojin yakinsu guda 16, kuma kowanne daga cikin kwamandojin an ware masa yankin da zai jagoranci hari
ga jerin sunayen kwamandojin kamar haka:
1. Ba’ana Damaturu
2. Sa’ad Fiyar
3. Mohammed Shuwa
4. Mohammed Idris
5. Khalifa Umar (sun nadashi sabon Alkali)
6. Baba Gana
7. Abu Rabe
8. Abdul-Jalil
9. Abu Abdullahi Imar
10. Ibn Umar
11. Bulama Musa Ingilewa
12. Hasana Ba Gana
13. Malam Mohammad sa’ad
14. Abakar Dan Guduma – Sabon kwamandan sojojin ruwa (Amirul Bahar)
15. Mankur Guduma
16. Malam Abdul-Malik

A cikin wadannan kwamandojin yakin ISWAP akwai Ba’ana Damaturu wanda anyi ikirarin hallakashi a baya, amma sai gashi bincike ya nuna mana an nadasu a matsayin sabbin jagororin yaki a daular ISWAP, cikinsu babu wanda bai je Kasashen Libya, Mali, Sudan da Algeria ya samu horo akan ayyukan ta’addanci ba, da wasu kasashen gabas ta tsakiya

Wato nayi bincike da nazarin abubuwa masu tarin yawa akan yaki da Boko Haram, ina yabawa kokarin da dakarun tsaron Nigeria sukeyi da nasarorin da suke samu a kan ‘yan ta’addan Boko Haram, amma yanzu shekaru 10 ana fafatawa da Boko Haram ba’a kai ga shafesu daga doron duniya ba, kuma akwai tsoron cewa Boko Haram sunyi sulhun boye da junansu

Duk wani ‘dan Nigeria da yayi karatu akan yaki (War studies) kuma yana bincike da bibiyan sha’anin tsaron Nigeria ya san cewa akwai banbanci da gibi sosai tsakanin dabarun yakin ‘yan ta’addan Boko Haram da na hukumomin tsaron Nigeria, dakarun Nigeria sun samo dabarun yakinsu ne da kuma horo daga Kasar Ingila wacce ta yiwa Nigeria mulkin mallaka

Sannan su kuma ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP sun samo dabarun yakinsu ne daga ‘yan tawayen Somalia da kuma Algeria, su kuma sun samu daga sojojin Afghanistan, wato ‘yan tawaye (Taliban/Al-Qa’idah), wanda su kuma wadannan kungiyoyin ‘yan ta’adda ko ‘yan tawaye sun samu horo ne da dabarun yaki daga sojojin tsohuwar daular tarayyar Soviet wato Kasar Rasha (Russia) a yanzu

Haka kuwa ya farune tun lokacin da Tarayyar Soviet tayi yunkurin mamayer Kasashen Afghanistan, Pakistan, Iraqi da sauransu, wanda a sanadiyyar hakane aka kafa kungiyoyin jihadi da kyakkyawan niyya don a kori Soviet tare da goyon bayan Amurka, bayan kammala yaki an kori Soviet sai kungiyoyin suka bada fatawar dabbaka jihadi a duk duniya, shine sanadiyyar wanzuwar kungiyoyin ta’addanci a wannan karnin da suka samu horo da dabarun yaki irin na Kasar Rasha

Abin nufi, dakarun tsaron Nigeria suna amfani da dabarun yaki irin na Kasar Ingila ne, su kuma ‘yan ta’addan Boko Haram suna amfani da dabarun yaki irin na Kasar Rasha, don haka akwai banbanci tsakanin dabarun yakin dakarun Nigeria da na ‘yan ta’addan Boko Haram

‘Yan ta’addan Boko Haram musamman ISWAP suna da kwarewa sosai a yakin Sahara (desert operation) yayin da dakarun Nigeria suna da kwarewa a yakin sunkuru (bush operation), sannan Boko Haram sun kware sosai a yakin tsakar dare, zasu iya shafe nisan dare suna yaki a cikin duhu babu haske wanda namu ba su kware a kan haka ba, sannan akwai abinda Boko Haram suka yarda dashi a bangaren yaki wanda masana tsaro a turance suke kira da (siege and operate) wato a gewayeku kafin a kaddamar muku da hari, Boko Haram sun yarda da wannan dabara na yaki sosai musamman da daddare, sai sunyi taking control a inda suke son suyi hari kafin sai su kaddamar da harin

A namu bangare; dabarun yakin Kasar Ingila da muke amfani dashi a Nigeria abinda ya yadda dashi shine (attack before operate) wato sai an kaddamar da hari kafin hari ya biyo baya, yawanci akan wannan dabarun yaki Ingila ta reni hukumomin tsaron mu

Ana cikin wani yanayi da sai Boko Haram sunyi hari kafin a mayar musu da martani, yayin da su kuma Boko Haram sai sun gewayeku kafin su kaddamar da hari, kuma suna da dabarun yakin da duk inda kaga ‘dan Boko Haram a fagen daga akwai wani a bayansa, idan ka bugeshi na bayan zai hauro ya maye gurbinsa, sai kaga kamar ba zasu kare ba, wannan dabarun yakinsu ne da ya sha banban da namu

Akwai wani abinda Boko Haram sukeyi a cikin dabarunsu na yaki, suna tafiya da rawani ko gammo su jikashi da ruwa da suke rufe fuskarsu dashi, wannan yana taimaka musu wajen hana tasirin hayakin hodar bindiga da zasu shaka ya cutar dasu, domin hayakin hodar bindiga guba ne, idan ana shakarsa yana dauke yawun baki ya haddasa bushewar makogoro, shiyasa duk tsawon lokaci da za’a dauka ana ruwan wuta Boko Haram ba zasu gaji ba, kuma Boko Haram ba su cika amfani da takalman da idan suna tafiya zaiyi kara ba, wannan dabaru ne na yaki a cikin duhu da suke yi

Don haka akwai bukatar hada dabarun yaki iri biyu ko sama da haka wa dakarun Nigeria, ana bukatar sabon training gaskiya, ta’addanci ya shigo mana, babu wanda ya san ranar da za’a gama ta’addancin, idan ana so aci nasara to dole sai an canza dabarun yaki an kawo kayan aiki na zamani, an kula da hakkin dakaru, sannan duk wanda aka sani yana da taimakon da zai bayar a yaki Boko Haram to a gayyatoshi, amma dole sai anyi tankade da rairaya, duk wanda bincike ya tabbatar maciyin amana ne a sallameshi

A nemo duk wasu kwararrun jami’ai a cikin kowace irin rundinar tsaro suke a Nigeria a shigar dasu cikin yaki da Boko Haram, ace kai je ka rike mana bangare kaza, wancan ma a ware masa nasa, a basu dukkan kayan aiki da suka bukata, a ayyana dokar tabaci akan iyakokin Nigeria da kasashen dake makwabta da yankin tafkin Chadi, inda halima a gina katangar karfe tsakaninmu da su, sannan a dauke network service kamar na tsawon wata biyu, duk wata kungiyar bada agaji idan ba na gwamnati bane a sallameta, a haramtawa ‘yan jaridu hanyar samun bayanai akan yakin, ayi amfani da wannan lokacin wajen shiga duk inda wata maboyar ‘yan ta’adda yake a Kasar Borno, Yobe da Adamawa ta sama da Kasa ayi musu kawanya da mamaya a kawar da su daga doron duniya

Idan ba’a shiryawa ‘yan ta’addan Boko Haram din nan da kyau ba to babu shakka su kam suna shiri, kuma sun tabbatar da cewa ko a kawo musu hari ko kar a kawo musu hari to su kam zasu kawo hari, kuma idan anki ji to ba za’a ki gani ba, ba zanji dadi ba ace shugaba Buhari ya kammala wa’adin Mulkinsa ya koma Daura yana jin labarin cewa Boko Haram suna cigaba da kashe mana ‘yan uwa da dakarun tsaron Nigeria, don haka Baba ya farga daga abinda yake faruwa

Yaa Allah Ka kawo mana karshen ta’addancin Boko Haram da masu tallafa musu ta kowace irin hanya Amin

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here