Waraka 6 Da Ke Tare Da Cin Dankalin Hausa

0

Waraka 6 Da Ke Tare Da Cin Dankalin Hausa

Kwararru da masana dankalin Hausa sun yi kira ga mutane da su yawaita cin dankalin ganin cewa yana dauke da sinadarorin dake kare mutum daga kamuwa da kowacce irin cuta a jiki.

A kasashen duniya da dama ana matukar noma wannan dankali saboda amfanin da yake dashi a jiki.

Wasu daga ciki amfanin da yake yi a jikin mutum sun hada da:

1. Yana kare jiki daga kamuwa da cututtuka.

Dankalin Hausa na dauke da sinadarin Vitamin B6 wanda ke kaifafa kwakwalwa, hana kamuwa da dajin dake kama jini, hana damuwa, kawar da laulayin haila da sauran su.

Dankali na dauke da sinadarin Vitamin C wanda ke warkar da mura, tari, warkar da ciwo ko rauni da sauran su.

Sannan yana dauke da sinadarin Vitamin D dake karfafa aiyukkan hanji, karfafa kasusuwa, hana kamuwa da dajin dake kama fata da sauran su.

See also  Taliban: Shari'a, Jahilci da Rashin adalcin Musulmi

2. Yana dauke da sinadarin Magnesium da Potassium

Sinadarin Magnesium na taimaka wa jikin mutum wajen hutu musamman idan an gaji, yana inganta bugawar zuciya, karfafa jijiyoyi, kasusuwa da sauran su.

Sannan Potassium na kawar da kumburin jiki, kawar da cutar koda, Kare mutum daga bugawar zuciya da karfafa jijiyoyi.

3. Dankalin Hausa na dauke da sinadarin Beta-carotene wanda ke karfafa ido da karfafa garkuwan jiki.

4. Dankalin Hausa na kawar da cutar siga.

5. Yana dauke da sinadarin Vitamin A wanda ke inganta karfin ido.

6. Yana kuma dauke da sinadarorin hana kamuwa da cutar daji kowace iri a jiki.

Daga: Gulmawuya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here