Yadda Man Darbejiya Ke Magance Cutar Sanƙo

0

Yadda Man Darbejiya Ke Magance Cutar Sanƙo

Itacen dalbejiya ko kuma dogon yaro ko ‘Neem tree’ a turance tana da daci amma tana da matukar amfani ga jikin mutum.

Ga wasu hanyoyi da amfani da dalbejiya ke yi a jikin mutum:

Ganyan dalbejiya na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawar zuciya musamman idan aka dafa ganyen ana shan ruwan kamar shayi.
Ganyen dalbejiya na taimakawa wajen tacewa da tsaftace jinin mutum a jikin sa.
Ganyen na maganin cutar zazzabin cizon sauro da Typhoid.
Yana kuma maganin cutar ciwon ciki musamman idan cikin mutum ya murde saboda wani abincin da aka ci.
Ganyen dalbejiya da man shi na gyara fatar jikin mutum.
Ganyen na maganin sanko, magance amosanin kai da kuma sanyawa gashi ya yi tsaho, ta hanyar shafa man dalbejiya a ka.
Ana iya amfani da man dalbejiya a matsayin dabarar bada tazarar iyali.
Ganyen na kawar da cutar daji musamman dajin dake kama nono, ‘ya’yan maraina sannan yawan amfani da ita na hana kamuwa da cutar.
Ganyen na maganin cutar gyambon ciki wato ‘Ulcer’ da kuma rauni a jiki.
Yana rage kiba a jiki musamman ga masu fama da ita.
Yana warkar da ciwon gabobi da ciwon kai.
Yana kare mutum daga kamuwa da cutukan da ake samu ta hanyar yin juma’i
Warkar da kuturta.
Yana maganin ciwon ido.
Yana maganin guba da ake samu daga jikin dabba kamar cizon cinnaka, maciji da sauransu.
Ganyen na maganin kwari musamman wadanda ke lalata amfanin gona.

See also  KATSINA, MA’AIKATA, ALBASHI DA CIWO BASHI

Mun Ciro daga shafin Gulmawuya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here