AN FASA WANI OFIS A SAKATARIYAR KATSINA?
Daga Taskar Labarai
Jaridar Taskar Labarai ta samo labarin cewa wasu da ba a san ko su wanene ba, sun fasa wani Ofis a ofishin sakataren gwamnatin Katsina dake sakatariyar Katsina.
Sun yi awon gaba da wasu kudaden da aka ajiye don tafiyar da ofis. Daya daga cikin editocin Taskar Labarai yaje har sakatariyar don binciken lamarin ya kuma tabbatar da faruwar lamarin.
Editan ya samu tabbacin har an kama wasu masu gadin an kuma gayyaci wasu ma’aikatan da lamarin ya shafi ofis nasu.
Akwai shaci fadi na yawan kudin da ake jin an dauka wanda taskar labarai bata tabbatar da yawansu, yanzu haka tana kan bincike akai.
Taskar Labarai ta tuntubi kakakin rundunar ‘yansanda ta jihar Katsina, yace bashi da masaniya amma zaya bincika.
Taskar labarai na bin diddigin labarin kuma zata ci gaba da kawo maku me ake ciki.
NB . Taskar labarai jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo a shafin www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta tana kuma da ta turanci mai suna the links news dake a www.thelinksnews.com 07043777779