BINCIKEN SHEKARU GOMA: ABUBAKAR BUHARI BAI KASHE MAHAIFINSA BA.

0

BINCIKEN SHEKARU GOMA: ABUBAKAR BUHARI BAI KASHE MAHAIFINSA BA.

Daga Danjuma Katsina

A shekarar 2010 labari ya watsu a jihar Katsina dama duniya cewa, wani yaro mai suna Abubakar Buhari dan shekaru 14 daga garin Kadandani karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina ya kashe mahaifinsa.

Labarin yace Abubakar ya sanya wa mahaifin nasa mai suna Malam Buhari shinkafar bera a abinci kuma yaci ya mutu, malam Buhari wanda yake ma’aikacin asibiti ne kuma yana da kusan shekaru 55 da a duniya.

”A ranar 26 /2/ 2010 nazo daga Katsina inda nake zaune mahaifina ya kira ni da cewa in zo dan yayi mani sayayyar tafiya makaranta, da yamma na shiga gida sai matar babana tace ga abinci babana in kai masa kofar gida, na fada mata daga wajen nake ba kowa ta tilasta in dau abincin inje in duba.

Na dauka naje na dawo nace ba kowa tace to ajiye shi, ina can wajen abokai na sai aka ce ga baba na can cikin sa ya kulle ina zuwa gidan da sauri sai kawai aka ce me ka ba baba?
Nace me fa na saka masa? Naji babana na magana na matsa kusa da shi sai ya rika ce mani Abubakar saboda kai akai mani haka kuma don Naji zan kara aure don Allah ta kowane hali ka zama mutumin kirki, in har sun barka ka rayu. Kafin kace me na rika jin bugu ko ta ina ”

Kadan daga abin da Abubakar ya rubuta a wani littafin da ya rubuta da yana gidan yari a tsare.

Hukumar ‘yansanda a lokacin ta gabatar da yaron ga manema labarai da sauran wasu masu laifi. Na je wajen a wancan lokacin kuma a nan naga Abubakar ina kallon shi na kuma yi magana da shi a kebe na kasa samun natsuwar cewa zai aikata wannan mugun aikin.

Amma bani da hujjar in ja da abin da ake tuhumar sa da shi, amma na daukar ma kaina bincike mai zaman kansa da bin diddigin rayuwar Abubakar a duk inda ake tsare dashi.

A wancan lokacin naje har Kadandani garin in da nayi magana da mutane da kuma ‘yan uwan mamacin. Amsar da na kasa samu ita ce da wane dalili Abubakar zai sanya ma mahaifinnsa guba a abinci ya kashe shi?

Abubakar shi ne babba da a wajen mahaifin sa Malam Buhari kuma yana son sa yana masa duk abin da yake so.

Malam Buhari na da mata wadda ba ita ta haifi Abubakar ba, kuma bincike ya tabbatar mani ba a ga maciji tsakanin Abubakar da matar uban sa .

Ko a lokacin bincike ya tabbatar mani marigayi Malam Buhari na shirin kara aure, don wasu dalilai na sa na cikin gida. A littafin da Abubakar ya rubuta ya nuna yadda har matar tayi yaji aka maido ta.

Lokacin da Abubakar na a wajen ‘Yansanda na rika tambayar ‘yansanda me zasu fadi a kan halayyarsa? Shin a cikin sell yana tarayya da masu miyagun laifi? Amsa ita ce a’a, kuma kullum maganar sa daya ce, anyi masa sharri ne.

An kai Abubakar kotu, aka tura shi gidan kangararrun yara, don a tsare shi har zuwa kammala shara’a. A gidan kangararrun yara na rika zuwa da kaina ina bin rayuwar Abubakar duk masu kula da gidan sun san cewa ni kadai ne ke zuwa wajen sa, duk ina bibiyar rayuwar sa, in ji ko yana haduwa da manyan masu laifi? Amsar daya ce Abubakar yaron kirki ne.

A dabi’ance inda yaron banza ne, yana shiga wajen tsararrru zai nemi ‘yan uwansa kangararrun don su kara gogewa.
Bayan na samu tabbacin wannan sai na fara bin ya za a taimaka masa? ta kafofin watsa labarai? Na samu ‘yan jaridu da dama cikin su har da Alhaji Habib Bello Usman na KTTV lokacin yana daraktan labarai da al’amurran yau da kullum na gidan talabijin na jiha.

Abubakar baya da lauya gashi yaro wani lauya ya daukar ma kansa kare shi kyauta bayan ya fahimci halin da yake a ciki.

“ranar da aka kaini gaban alkali, ya duba ni yace kana da lauya nace bani dashi yace me kake so nace ayi mani adalci” a littafin da ya rubuta.

Anyi ta shara’a har shekaru biyu, lauyan da ya tsaya masa yayi iyakar kokarin sa, hatta alkalin ya fahimci halin da Abubakar ke ciki, amma Alkalai na hukunci ne da hujjar da masu gabatar da kara suka gabatar masa, da kariyar da masu kare mai kara suka iya karewa.

“Da aka aika dani gidan yari alkalin ya rubuta a takardata cewa, kar ka hada wannan yaron da manyan masu laifi nan na gane alkalin na tausaya mani ba yadda ya iya saboda hujjojin da aka kawo masa “” inji Abubakar a littafin shi.

A lokacin gidan yari shi ne wuri mafi sauki ga Abubakar a halin da yake a ciki. Baya da kowa a duniya an kuma bata masa suna kowa na gudun shi don haka alkalin ya yanke masa hukunci, a ranar 1/11/2012 na shekaru Goma a gidan yari. Kasancewar sa yaro lokacin yana da shekara 16 a duniya, ba a iya yanke masa hukunci na kisa ko daurin rai da rai ba.

Ko a lokacin wani abu da na lura da shi shi ne, a lokacin binciken cewa me ya kashe Malam Buhari mahaifin Abubakar ba wani bincike da aka yi na abincin, guba ce? Wace irin guba ce? Ba binciken da aka yi ma jikin mamacin, kuma ‘yansanda basu tuhumi kowa ba basu kuma binciki kowa ba.

Abubakar kadai aka zarga shi ne kadai aka tuhuma shi kadai aka bincika kuma shi aka gabatar gaban kotu.

“ina shigowa gidan akace kaine kasa wa baba guba nace guba akan me da wane dalili ? Sai na nufi inda babana yake juye-juye cikin sa na ciwo”.

Wanda a ka’ida kamata yayi duk kowa ya zama abin zargi tun daga matar mamacin har zuwa sauran ‘ya’yan sa, ayi masu tuhuma da binciken duk abin zargi ne har sai binciken ya wanke su.

Abin da ba a yi ba kenan a lokacin. Abubakar kawai aka zarga kuma aka tuhuma aka bincika aka kuma kai kotu aka yanke ma hukunci.

A zaman kotun duk wadanda suka bada shaida akan tuhumar mutane da suke da danganta ta kusa da matar mamacin wadda ita ma ya kamata ace an tuhume ta don ita ta dafa abincin da aka ci. kamar yadda na gani a jawabin shara’ar dake adane a kotun.

“cikin wadanda suka bada shaida har da mahaifin matar babana, sai wasu ‘yanuwan mahaifina amma suna kusa da ita sai takardar da na sama hannu a wajen ‘yansanda wanda azaba ta sa na saka hannu”

Kafin yanke hukuncin, duk wadanda sukayi mu’amala da Abubakar sun fahimci lamarin yana da sarkakkiya kuma sun tausaya masa, amma a yanayin da ake cikin lokacin zaman gidan yari ga Abubakar shi ne mafi maslaha ga shi da rayuwar sa, kamar yadda a lokacin ake shaida mani ga duk wanda na tuntuba.

Bayan an yanke masa hukunci an kai Abubakar gidan yarin Katsina nan ma na rika bin rayuwar sa. Wadanda mazauna gidan suka shaide shi akan baya hudda da duk wasu masu laifuka. Yaron kirki ne, duk gidan. Daga baya aka mai da shi Kaduna gidan kangararrun yara a can Kaduna wajene da ake kai masu laifin da shekarunsu bai kai na zama gidan yari ba.

A nan ne ya rika karatun addini ga wasu da ake tsare dasu tare kuma ya koyi sana’ar dinkin keke . Nan ma an yi masa shaidar kirki daga baya da shekarunsa suka kai aka maido shi cikin gidan yari.

A babbar gidan yarin Kaduna an sanshi da Abubakar tela, don yana kara kwarewa a sana ar dinkin keke, kuma yana yiwa wadanda ake tsare dasu da ma ma aikatan gidan dinki, nan ma anyi masa shaida da yaron kirki.

A zaman sa, bai yarda ya biye ma bata gari ba, ya rika cewa an mani sharri ne don a halaka ni ko kuma in lalace, nayi ma Ruhin mahaifina alkawali sai na zama mutumin kirki don in rika yi masa addu’a da iyalina in Allah yaso.

A gidan yarin Kaduna manyan masu laifi sun yi kokarin jawo shi jikinsu suna nuna masa ya shiga cikinsu su daukar masa fansa yaki amincewa. Duk gidan yarin Kaduna anyi ma Abubakar tela kyakykyawar shaida.

Abubakar ya rubuta littattafai guda uku a gidan yari cikin su akwai daya Wanda ya bada labarin daki-daki abin da ya faru har zuwa lokacin da yake saura watanni kadan ya fito.

A littafin Wanda jaridar Taskar Labarai zata dau nauyin bugawa da watsa shi a cikin Al’umma. Kuma za a buga shi da harshen turanci, Ya bada tarihin mahaifin nasa da kusancinsu da yadda suka shaku dashi, da rayuwar gidan mahaifin nasa, da kuma irin azabar da ya rika sha wajen matar babansa mai suna Halima.

A littafin ya kawo daki-daki dalla-dalla me ya faru akan zargin da aka tuhume shi da shi? Da azabar da yasha wajen tambayoyi a wajen ‘yansanda da ta sanya har ya sa hannu a takardar tuhumar. A tsanake ya rika kawo me ya faru.
Har zuwa yanke masa hukunci. Da kuma rayuwar sa a gidajen yari da ya zauna har guda hudu. Rubutu ne mai ban tausayi da ratsa zuciya.

An saki Abubakar Buhari a watan Yuli na 2019 bayan ya gama shekarun hukuncin da aka yanke masa.
Yana fitowa ya nufo Katsina, yaje ya ga gidan mahaifin shi, ya kuma shiga garin Kadandani ya rika gaisuwa da mutane, yana kara jaddada cewa shifa sharri ne aka yi masa. Ya kuma je kauyen da Mahaifiyara a can cikin garin charanci ta ke aure ya same ta a karon farko taji daga bakin shi, tayi farin ciki cewa ta gamsu danta sharri aka yi masa.

Amma illa ta riga ta faru don kuwa lokacin da yana tsare mahaifiyarsa ta samu ciwon hawan jini saboda da damuwa, kuma shi ne yayi sanadin rasuwarta a a watan Janairu na 2020. Yanzu Abubakar ba uba ba uwa.

Abubakar ya dawo cikin birnin Katsina yana yawon sana’arsa ta dinkin keke. babban hatsarin da yake fuskanta ‘yan uwansa na neman su cutar da shi don haka yana kauce ma ganin su a kebabben wurin da ba kowa. Fatan sa a buga littafin da ya rubuta duniya ta fahimci daukar Alhakin sa da akayi.

Duk rayuwar Abubakar a gidajen yari bai yarda rayuwarsa ta gurbata ba.yace alkawali ne yayi ma Ruhin mahaifinsa.

“dangi da ‘yan uwa su sani bani na kashe mahaifina ba kuma zan ta magana har Allah ya bayyanar da gaskiya” inji shi a wata zantawa da marubucin nan yayi dashi.

Danjuma Katsina marubuci kuma Danjarida mawallafin wasu jaridun yanar gizo ne jaridar Taskar Labarai da kuma The Links news 08035904408 email mdanjumakatsina@gmail.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here