HARI A MAGAMAR JIBIA CIKIN DAREN NAN

0

HARI A MAGAMAR JIBIA CIKIN DAREN NAN
Daga taskar labarai
Mahara sun kai farmaki a garin magamar jibia ta karamar hukumar jibia jahar katsina a daren yau Talata.
Tun karfe bakwai na yamma aka ga maharan bisa babura su Goma sha tara da makamansu rataye dai dai koramar garin.
An gansu suka ajiye baburan suka tako kasa suka Dan shigo gari sukayi hidimarsu suka koma suka dau baburansu.
Karfe Goma na dare nayi suka bullo ma garin ta duk bangarorin ko ina suna harbe harbe.da darko mutane sun tsorata.
Amma daga baya suka fito suka fuskanci maharan, wannan ya jawo suka bar garin ba shiri.
Wajen fafatawa da mutanen har sun harbi mutane wadanda ba a tantance yawansu ba.babu tabbacin ko sun tafi da wasu.ko wani
Daga baya soja da yan sanda sun kawo ma mutanen garin dauki.kamar yadda ganau ya tabbatar wa da jaridar taskar labarai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here