SARKI QABUSU NA KASAR OMAN: TURKEN ZAMAN LAFIYA A GABAS TA TSAKIYA

0

SARKI QABUSU NA KASAR OMAN: TURKEN ZAMAN LAFIYA A GABAS TA TSAKIYA

Daga Danjuma Katsina

Wani karatu da na taba yi, na yi rubutu a kundin kammala karatun na yi ne akan sarkin da kuma kasar sa ta Oman.
Karatu ne akan siyasar kasa da kasa da kuma tattara bayanai sirri don amfanin zaman lafiyar kasashe.

Sarki Qabusu yayi karatu a kasar Ingila tsakanin 1958 zuwa 1960 a lokacin jami’an sirri na burtaniya suka horas da shi don amsar gwamnatin kasar ta Oman da mayar da kasar wani sansanin tattara bayanan sirri na su.

Bayan ya gama karatun shi, ya dawo sai mahaifinsa ya lura da taketakensa, wannan ya sanya ya sa aka tsare shi a gida baya fita ko’ina sai da dalili.

A tsaren da taimakon jami’an tsaron Burtaniya yayi ma mahaifinsa juyin mulki ya hau karagar mulki a 1970.
Yana hawa aikin farko da ya far shi ne gamawa da ‘yan tawayen markasanci dake kasar sa. Da taimakon kasar Iran, Jordan da Burtaniya.

Ya gina kasar sa a gabas ta tsakiya akan bata shiga harkar kowace kasa, duk maganar da zasu shiga to ta neman sulhu ce da fahimta.

Lokacin yakin Iran da Iraq duk kasashen Larabawa sun goyi bayan Iraq, Oman ce kawai ta dau matsayin ‘yar ba ruwanmu kuma ta taka rawa sosai na kawo sulhu.

Ita kadai ce, bata da wata kasa abokiyar gaba duk duniya, duk lokacin da kasar Iran ta kafe a wata matsaya sarki Qabusu ne kawai ke shiga tsakani kuma ayi nasara.
Kasar ta zama wani sansani na tattara bayanan sirri kasashe, amma tana zaune lafiya kuma bata komai da zai hada ta fada da wata kasa.

Ta samu cigaba inda ilmi kyauta ne har digrin-digirgir, lafiya ma kyauta ce. Musulmi ne kashin casa’in bisa dari, mabiya sunna da wata mazhaba da suke kira ibadi. Wanda duk duniya su kadai ke bin mazhabar, sai mabiya shi’a. Akwai kiristoci da Yahudawa baki a kasar.

Kasar na da yawan mutane miliyan hudu da ‘yan kai.
Sarkin bai taba haihuwa ba, yana ji da sarautar ya taba daukar shekaru biyar bai taba magana ba sai dai ace yace. Cutar kansa ce ta zama ajalinsa.

Danjuma marubuci ne kuma Danjarida ana iya samunsa a 08035904408

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here