JAMI’AN APC DA ‘YAN NEMAN TAKARA A KATSINA

0

JAMI’AN APC DA ‘YAN NEMAN TAKARA A KATSINA
~~~ SHARHIN TASKAR LABARAI

Wasu hoto na da ya karade shafukan sada zumunta kwanan nan ya tada muhawara a gidajen masu neman takarar gwamna a 2023 jihar Katsina.

Hotunan guda hudu ne daya na Alhaji Shitu S Shitu shugaban jam’iyyar APC a jihar Katsina na jawabi wani matashi na masa dogari.

Wanda ke masa dogarin da riga da hula ta tallata wani da ake ganin yana son takarar gwamna a 2023. Wasu hotunan kuma na wasu makusantar shugaban jam’iyyar ta APC ce sanye da wadannan huluna da riga.

Wani hoton kuma ya kawo yadda aka ga shi wancan da ake ganin yana fatar takara yana kaddamar da irin wadannan riga da hula.watau sakataren gwamnatin Katsina, Alhaji Mustafa Muhammad Inuwa.

Wani hoton kuma ya rika yawo na wani taro da aka yi a lahadin da ta wuce a dakin taro na cibiyar horas da sana’o’i dake Filin Samji. Taro ne da aka yi don yada da kuma tallata muradin wancan da ake ganin yana shirin takara a 2023. Sai ga jami’in hudda da jama’a na jam iyyar APC a cikin manyan baki, Alhaji Abu Gambo yana teburin masu gudanar da taron.

Wadannan hotuna sun zama abin magana a gidajen da suke neman takarar gwamna a jam’iyyar APC a katsina. Kusan dukkanin su na ganin kamar jami’an jam’iyyar sun dau wani matsayi tun ba a je ko ina ba, wanda kuma suna ta tattauna matakin da za su iya dauka in hakan ta tabbata.

Mu a Taskar Labarai muna ganin cewa ya kamata shugabannin jam’iyyar APC ta Katsina su sani akwai dangantaka ta kusancin daidaiku akwai kuma ta nauyin ‘yan jam’iyya baki daya. Wadda kuma jam’iyyar nan ita ke mulki don haka, akwai nauyin Al’ummar Katsina baki daya.

Muna ganin su rarrabe wannan kuma kar su cusa dangantakar su ta shafi jam’iyya da ‘ya’yanta, wanda zai shafi Al’ummar jaihar.

Su sani cushen dan neman takara ga mutane kamar hadiyar kwayoyin cutar Sankarau ne, don haka ya kamata su yi ma kansu Kiyamullaili. su tsaya a matsayin su na shugabanni. Kuma su rika taka tsantsa. In wasu jama’a zasu yi, wannan ‘yancin su kuma suna da damar haka amma a bar wayon shigo da jami’an jam’iyya.

Su sani dimokaradiyar mu ta fara balaga jama’ a sun fara wayewa a siyasance duk wata Kunshe ko Sake, kar suke kallonsa kuma za su botsare in lokacin yayi.

mu a Taskar Labarai zamu saka ido, muna ji muna gani muna kuma saurare, za kuma mu fadakar da Al’umma ga duk abin da muka fahimta za a kauce.
________________________________________________
Taskar labarai jarida ce mai zaman kanta da ke bisa yanar gizo www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta tana da ‘yar uwarta ta Turanci mai suna The links News dake a www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta. Kira ko sakon gaggawa 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here