ALLAH TSARE MU DA KAMBIN BAKA, SOKE , HAU DA SAURAN SHARRUKA.

0

ALLAH TSARE MU DA KAMBIN BAKA, SOKE , HAU DA SAURAN SHARRUKA.

Daga Danjuma Katsina

Kamar yadda akwai ciwuka na jiki, irinsu masassara da ciwon kai da sauransu. hHaka ma akwai wasu masifu da suka danganci rayuwar Dan’adam wanda da yawa mutane basu sani ba, kuma suna da tasiri a rayuwar Dan’adam.

Wadanda suka rayu a gidan malamai na Allah sun san irin wannnan ilmin, zan kawo wasu daga cikin su.

KAMBIN BAKA: wata cuta ce da mutum yake bukatar neman tsari daga masu shi. Wasu mutane na da wani bala’i tare dasu. Duk abin da suka yi ma mummunar fata sai abin da suka nufa na muni ya bishi.

SOKE: Shi kuma wata cuta ce da akan nufa akan mutum duk abin da ya sanya gaba baya nasara, misali in Dankasuwa ne na bukatar jarin dubu goma ka bashi miliyan zata lalace, a hannun wanda akayi ma wa.

HAU: shi ne wanda in aka yi wa mutum shi, zai rika aikin da zai zubar masa da mutum ci. Har ya kai da kansa ya yi aiki da ya kai shi ga halaka ko tafiya gidan yari,na tsawon lokaci.

DINDIMI: Sirri ne na mutanen India shugaba ake ma shiin ya hau mulki ba zai taba farin jini ga jama’arsa/na taba rubutawa a jaridar Almizan cewa, an yi wa gwamnatin Shema irin shi a lokacin. kanun labarin shi ne: Anyi wa Gwamnatin Shema Sirrin Danmadindimi, ya fito a fuskar farko na jaridar.

See also  wasikar da farfesa sani Abubakar lugga ya rubuta ma masauratar katsina,

BIBIKO: shi kuma sirri na mutanen Malesiya ana yi ma masu mulki shi ne don su rasa madafa a mulkinsu, kullum su rika abin da bai dace ba, kuma suna cin fargar jaji.

DUHU: wani sihiri ne dake sama mutum shakku ga duk wanda ke neman zama da shi tsakanin shi da Allah amma ya rika jawo miyagu kusa da shi.

Cutukan suna da yawa a kundin bincikena, na samu sun kai kala ashirin da bakwai, kowane irinsa da yadda yake da alamominsa ga mutum wasu da yadda ake maganin su. Ko yadda ake tsare kai daga gare su, wasu ma da yadda ake yin su ga wanda aka nufa.

Misali DINDIMI da jaba da idon mujiya da fatar kulba ake hadawa, ayi wasu aiki na halaka da rabuwa da Allah . Ciwon sai yayi shekaru goma a jikin wanda aka nufa. Allah ya kiyaye mu Allah tsare mu Amin.

Danjuma Katsina shi ne mawallafin jaridun Taskar Labarai da The Links News da suke bisa yanar gizo da sauran shafukan sada zumunta. Www.taskarlabarai.com da www.thelinksnews.com 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here