JAM’IYYAR PDP A KATSINA NA HAYAKIN KAMAWA DA WUTA

0

JAM’IYYAR PDP A KATSINA NA HAYAKIN KAMAWA DA WUTA

Daga Taskar Labarai

Wasu abubuwa da ke faruwa a jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina na iya zama wata wuta da za ta kama jam’iyyar.

Wani da ya taba takarar gwamna a jam’iyyar mai suna Ahmad Aminu Yar’aduar yayi wani rubutun da ake yawo da shi a shafin sadarwa na zamani ( social media).

In da a rubutun yake cewa jam’iyyar PDP sai gyaran Allah in da ya yi zargin cewa jam’iyyar ta kasa nasara a jihar a zabubbukan 2015 da 2019.

Ya kuma yi zargin sun kasa cin zabubbukan cike gurbin da aka yi a Jibia, Katsina da Mashi da kuma Sanata na Daura.

Inda yace laifin na shugabancin jam’iyyar ne. Ahmad Aminu Wanda tsohon sakataren gwamnatin Katsina ne, yace shugabanin basu san kome ba sai yaudara da jari hujja. Ya kuma zargi shugabannin yanzu sun korai da ga jam’iyyar.

Ahmad Aminu yayi kira da rushe shugabancin jam’iyyar a nada mata na riko a dau wata shidda ko shekara a kasa sannan a yi zabe.

A wata sabuwa kuma wata kungiya da ta kira kanta ‘yan PDP masu neman gyara sun yi kira ga uwar jam’iyyar da ta shigo cikin abin dake faruwa a Katsina.

Kungiyar wadda shugaban ta Alhaji Abdul’aziz Kafin soli da yayi magana a madadin ‘ya’yanta ga manema labarai.

Yace sun aika da wata takardar korafi ga uwar jam’iyya akan yadda jam’iyyar take a jihar Katsina kuma sun yi kira ga uwar jam’iyyar da su rushe shugabancin ta a matakin jiha a nada na wata shidda kafin ai zabe.

Shugaban jam’iyyar na jiha Alhaji Salisu Yusufu Majigiri a wata magana da yayi da jaridar Daily Trust yace su wadancan masu korafin bai san dasu a jam’iyya ba. Kuma basa a cikin wani bangare na jam’iyya Wanda tsarin mulki ya san da su. Yace kowa na da ‘yancin fadin albarkacin bakin shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here