YADDA NA KUBUTA DAGA HANNUN MASU GARKUWA DA MUTANE.

0

YADDA NA KUBUTA DAGA HANNUN MASU GARKUWA DA MUTANE.

Daga Taskar Labarai

A ranar 08-01-2020 ne akayi garkuwa da Jami’an kwastam biyu tare da wasu fasinjoji dake cikin wata mota kirar Golf ciki kuwa har da direban motar mai suna Alhaji Bishir.

Da yake shi da jami’an kwastam sun dorasu kan babura ne suka shiga da su daji, fasinjoji kuma aka kora su kasa, amma sun kubuta sanadiyar jirgin Jami’an tsaro da yazo ya tarwatsa ‘Yan bindigar.

Da suka isa da shi dajin sun daure shi a jikin wata itaciya da sarka suka kwadduna suka kulle. Yan uwansa sun kira domin neman yadda za a sake shi, suka ce sai an basu naira miliyan hamsin (N50m), kam-kama dai aka basu naira dubu dari (N100,000), suka amshe kuma suka ki sakinsa.

A ranar 16-01-2020, da misalin 10:00pm sai suka ji karar tafiyar wani abu ya tunkaro inda yake daure, sai daya daga cikin masu gadinsa yace minene ya tunkaro mu haka? Sai Dan uwansa yace jakai ne suka dawo kiwo, sai yace kila dai rakumma ne suka dawo, da dai suka ji basu gamsu ba sai suka haska da fitila, kawai sai ga wasu irin manyan macizai bakake guda biyu sun tunkaro su, suka yi tsalle cikin tsoro, daya ya jawo mabugi ya tunkari macizain nan suka ruga ya bisu, amma sun fada wani rami, sai dayan da yake yafi tsorata yaje ya dauko bindiga domin ya harbe su kafin ya iso sun buya.

Can kuma sun dan kwanta sai macizain nan suka dawo, sai masu gadinnan suka tashi cikin matsanan cin tsoro daya ya yi ta maza ya bisu ya samu ya kashe daya can kuma sai suka rika jin kukan wani naman daji, suka ce wannan kuma kukan minene, sai yace masu kukan dila ne suka ce yana cizo yace kwarai kuwa, daya daga cikinsu yace shi dai gaskiya ba zai iya cigaba da kwana nan ba, kada wani abu yazo ya kashe su.

Nan dai suka yi ta Y’yan shawarwarinsu har suna cewa an ya ba yasin kayi mana ba? Yace ta yaya zan yi maku yasin? Ni da ke daure sallah ma kun hana in yi, da dai gari yayi buji-buji sai suka ce zasu je su sanar da manyansu cewa su baza su iya ci gaba da kwana wajen nan ba amma sai yace to su dan sassauta masa daurin domin ya bashi damar yin yar tafiyar koda kafa bakwai ce (daurin talala), bayan sun yi masa daurin talala sun tafi su kai korafinsu wajen manyansu, sai ya tashi ya zagaya ya samu wani dutse ya balle kwado daya, sannan sai ya tuna yaga inda suka ajiye gudan makullin sai ya tashi yaje ya laluba cikin kasa ya dauko shi yazo ya bude, sai ya tattara sarkar ya saka cikin wani buhu da suka bashi domin ya rika lullube kafarsa saboda sanyi, ya dauka yace kafa mi naci ban baki ba.

Ya yanko daji ya yi tayi baya bin hanya sai ratse domin gudun kada su biyo sawu ko kada ya hadu da wasu irinsu. Yana cikin tafiya idan ya karar babur sai ya lafe sai ya wuce ya ci gaba tun kafe goma na safe har karfe hudu na yamma, tafiya yakeyi babu alamum karkara, can sai ya hangi wani gidan fulani yayi kamar yaje ya roke su ruwan sha ya guji kuma kada a koma yar gidan jiya, ya dai za gaye yayi ta tafiya.

Sai kuma ya hangi wasu buzaye suna duban ruwa a wata rijiya nan ma dai ya labe ya zagaye masu, ga yunwa, kishiruwa, da matsanan ciyar gajiya can sai ya hangi wata primary a wani kauye sai ya isa ya duba ya leka bai ga kowa ba, duk gari sun tashi ba kowa, sai ya hangi wani dan acaba ya dauko wani soja, yayi ya tsaida su amma ina kodan suka hange shi sai suka kara wuta, sai ya fita ya kama hanya ida yayi kicibis da wani allo (symbo) wanda a jikinsa wata kibiya ta nuna hanyar gurbi wata kuma Shimhida, sai ya kama hanyar Shimhida, daga bisani sai yaga wani mai babur ya dauko wata mata ya tsaida shi ya shaida Masa halin da yake ciki, sai ya dauke shi ya kaishi Shimhide wajen shugaban Yan banga shi kuma ya kaishi wajen sojoji, su kuma suka kawo shi gida domin gudun kada su biyo sawu su sake kama shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here