YAN BINDIGA SUN YI GARKUWA DA MUTUM 11, A WANI KAUYEN BATSARI.

0

YAN BINDIGA SUN YI GARKUWA DA MUTUM 11, A WANI KAUYEN BATSARI.

Daga Taskar Labarai

A ranar talata 21/01/2020 da misalin karfe 12:00am Yan bindiga suka yi wa kauyen Yan-gayya dake cikin yankin karamar hukumar Batsari kawanya, suna shiga garin suka yi ta harbi ba kakkautawa.

Haka kuma sun rutsa da mutane suna hira wurin wani mai shayi, take suka ce duk wanda ya motsa zamu harbe shi, amma dai duk da haka wasu suka yi ta maza suka rankaya a guje domin su tsira.

Sauran kuma suka yi ciki dasu. Lokacin da suke kara-kaina cikin garin sun yi kicibis da wani Mallam Hamisu, suka tambaye shi namu ne ko nasu, da dai suka fahimci ba nasu bane, sai kawai suka harbe shi harbin rashin imani, a kai da ciki, hanji da kwalwa waje, hakan yasa take Allah ya karbi abinsa.

Daga nan kuma sai suka fada gidan Alhaji Mu’azu (wani dattijo) inda suka taradda jikokinsa suka yi awon gaba da su, sannan suka juya kansa suka dora masa bindiga suka ce ya basu kudi ko su kashe shi, ya lalubo yar jikkarsa ya mika masu kudinsa dubu ashirin sannan suka kyaleshi.

See also  Kungiyar IPMAN Ta Ce Farashin Litar Mai Ba Zai Yi Kasa Da Naira 500 Ba

Daga bisani suka tattara mutanen da suka kama suka kora su kasa, sai da suka yi nisan 2km sannan suka isa inda suka ajiya baburansu suka dorasu.

Amma daga bisani wani daga cikin wanda aka yi garkuwa dasu ya kubuta sakamakon baya iya tafiya sai suka yi masa duka sannan suka kyaleshi ya rarrafa ya isa wani kauye da ake cema Duba, daga nan ne aka dauke shi zuwa babbar asibitin Batsari.

Ga sunayen wadanda akayi garkuwa da su:

1.Aminu Maikudi
2.Muhammadu Usman
3.Abubakar Hassan
4.Ayuba Yusif
5.Sadiku Bala
6.Abubakar Habibu
7.Mallam Hamisu mai sitika
8.Dan Autan goro
9.Kabir Hassan
10.Rabe Na-Mansir
11.Hassan Geji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here