Kyakkyawar Bafulatanar Da Ta Jefa Kanta Cikin Harkar Garkuwa Da Mutane

0

HAUWA YUNUSA: Kyakkyawar Bafulatanar Da Ta Jefa Kanta Cikin Harkar Garkuwa Da Mutane

Daga Shuaibu mai Swansea

Hauwa ‘yar shekaru 24 kacal, amma kwararriya ce wajen fashi da makami, garkuwa da mutane da aikata kisa. Ta yi aure sau uku, tana rabuwa da mazajen saboda rashin jin maganarta.

‘Yar asalin kabilar Fulani ce wacce take zaune a garin Masaƙa dake jihar Nassarawa amma haifaffiyar jihar Jigawa.

Ita ta shirya yadda aka yi garkuwa da samarinta guda uku, inda suka biya kuɗin fansa. Saurayinta na farko ya bada miliyan biyu bayan aka ba ta dubu dari biyu, bayan ya kwashe kwana biyu a hannun abokan aikata laifin nata, shi kuma na biyu ya biya miliyan daya, inda aka ba ta naira duba hamsin, na ukun kuma ya bada dubu dari biyar saboda a cewar ta shi ba mai kudi bane.

Duk waɗan nan kuɗaɗe basu ishe ta ba, hakan ya sa ta hada baki da abokan ta’addancinta suka sace kawar ta mai suna Zainab saboda ta ji abokiyar tata tana faɗin cewa an turo mata da kuɗi har N600,000.

A dalilin wannan Zainab ta rasa ranta saboda tsantsan wahala da ta sha, sai Hauwa ta je dakinta ta dauki ATM din Zainab da nufin ta kwashe duk kuɗin dake cikin asusun ta, sannan ta sauya wa motar Zainab fenti sannan ta sayar da ita, kazalika ta sayar da dukkannin kayayyakin da marigayiya Zainab ta mallaka.

Hauwa dai a halin yanzu ta shiga hannu kuma ƴan sanda tun farkon shekarar da ta gabata, suna gudanar da bincike a kanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here