KATSINA ZUWA KANO: WANNAN TATTAKIN BA ABUN KOYI BANE

0

KATSINA ZUWA KANO: WANNAN TATTAKIN BA ABUN KOYI BANE

Sharhin Taskar Labarai

Wani matashi daga jihar Katsina dan asalin karamar hukumar Batsari yayi ikirarin wai ya yi tattaki daga Katsina zuwa Kano a kasa don taya gwamnan Kano Ganduje murnar nasarar da ya samu a kotun koli.

Matashin wanda ya bar Katsina a kasa ranar juma’a, inda ya gana da wasu marubuta a yanar gizo yayi hira dasu sannan ya fara tafiyar tasa.

Zuwa kafin rana ta fadi ya kai garin Kankia, wanda wannan ya fara jefa shakku anya a kasa a ka yi tafyar? Kuma anya babu hadawa da maganin kara kuzari? Abin da yafi ba kowa mamaki shi ne karfe takwas na safe har ya mike kuma an ganshi akan hanya zai nufi Kano kafin hudu na yamma ya kai garin tsanyawa a cikin jihar Kano.

Zuwa yamma ya sake dorawa ya kwana a garin Danzabuwa, wanda wannan tafi kama da an fara takawa tsakani da Allah. wan shekare kuma ya isa Bichi, wanda duk abin amincewa ne da yadda.

A lissafin hankali, an fara wannan takawa ne tsakani da Allah daga garin Tsanyawa, sauran kuma sai an yi bincike ko kuma mai tattakin ya rantse da Allah ba maganin shan kuzari ba ko kuma ‘yar dabara.

Kowa na da abin da in yaga dama zai yi da ransa yayi, ba tare da ka hana shi ba, kuma abin da matashin yayi bai sabawa doka ta kasa ba, kuma a ganin Taskar Labarai ba haramun bane, bukatarsa ce, son ransa ne, ganin damar shi ne , amma a ganin Taskar labarai ba abin kwaikwayo bane. Duk abin da matashi zai yi ya fara Sanya mutumcin aikin da kuma kanshi farko.

Katsina na da matasa zakakurai abin kwaikwayo a adabi, magana, kimiya da kuma siyasa da sauran bangarorin rayuwa. Amma sam ba irin na tattakin Katsina zuwa kano ba.

Kadan daga cikin matasan Katsina abin misali da kwaikwayo, akwai, irin su Malam Lukman Umar Kankia matashin da ya rubuta littafin hikaya na Turanci mai magana akan halin da kasar mu ke ciki, irin su Saifullahi Mato Kankara, wanda da taimakon rubutun shi na rashin tsoro aka kori PDP a Katsina, yanzu haka kuma akan halin da tsaro yake a ciki ya samo wata fasaha wadda in aka saurare shi zata yi amfani, a arewacin kasar nan baki daya.

irin su Yakubu sabo Musa wani matashin da duk gwagwarmayar ANPP zuwa APC a Katsina da su aka yi tun 2013 yana cikin manyan ta a yanar gizo da fasahar zamani . Irin su Kabir Bahaushe Dandagoro Wanda muryarsa a gidajen rediyo ta zama abin son aji kuma ya zama tauraro a MC.

Hatta wasu matasa da suka mayar da tallata duk wanda ya gayyace su a yanar gizo abin koyi ne. . irinsu yan biyu masu yiwa addini hidima hassan da husaini wadanda aka sani da HK Yar’adua TV online. Suma abin koyi ne, irinsu M k Aminu wanda kullum shafinsa na Facebook yana neman masu matsala ne yana neman masu taimako. Kuma aikin shi yayi sanadin taimakon mabukata da yawan gaske, wanda abin burgewa ba a taba jin an samu coge ba ga kokarin nasa ba. Irinsu Mai iyali Dan Musa da suka tsaya da dakewa tallata jam iyyar adawa da ya yanta.

Hatta kafofin mu na yanar gizo a katsina, wasu da muke dasu duk matasa suke mallake su, watau irinsu CLiqq Magazine ta jamilu mabai da kuma Katsina Post. ta mustafa Da Jakadiya TV and Redio ta Dan abba da Gobarau TV.ta yaseer

Wadannan kadan ne daga matasa abin koyi a Katsina, wannan ba a ma, kawo wasu da suka yi Zarra a kirkira ko ilmi ba.

Mu a Taskar Labarai muna rokon kar matasan su kalli wancan Dan tattaki abin wani kyakykyawan misali ko kwaikwayo, amma su su kalli misalan irin wadanda muka zayyano. Allah ya sanya a gane. Amin
…………………………………………………………………….
Taskar Labarai Jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma ‘yar uwarta ta turanci mai suna Www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here