TATTAKIN DAN BATSARI ZUWA KANO: DAN MAJALISAR JIHA KA KWAFSA

0

TATTAKIN DAN BATSARI ZUWA KANO: DAN MAJALISAR JIHA KA KWAFSA

Sharhin Jaridar Taskar Labarai

Wani matashi daga karamar hukumar Batsari dan shekaru 33 da yayi ikirarin tattaki daga Katsina zuwa Kano a kasa don taya Ganduje murna, ya isa lafiya, kuma har ya ziyarci mataimakin gwamnan Kano a Ofis nashi. Hausawa na cewa ‘shan koko bukatar rai’.

Wani abin takaici da aka nuno kuma aka yada yana yawo shi ne yadda aka ga dan majalisar jiha daga karamar hukumar Batsari na magana a gaban mataimakin gwamnan na Kano, kalmomin da kuma jadawalin jawaban sam ba a nan ya kamata yayi su ba, kuma maganganun kamar hannunka mai sanda ne ga gwamnan Katsina, wanda dan majalisa jiha yaje wata jiha yana fadar su.

Mu a Taskar Labarai mun lura cewa yankin sa na Batsari na cikin wadanda yafi fama da ibtila in hare-hare na ‘yan bindiga a jihar Katsina.

Da yawa mutanen sa sun yi gudun hijira zuwa birane kauyuka da yawa sun rauraye a yankin kafin kokarin gwamnatin jiha ta kawo abin ya yi sauki.

Binciken mu ya tabbatar mana mafi yawan zaman da aka rikayi na neman kawo gyara da sulhu a yankin babu hannun dan majalisar, Wadanda suka yi ruwa da tsaki sun tabbatar wa da jaridar nan haka.

Mun tabbatar hatta yawon da gwamnan Katsina yayi a daji don ganawa da barayin daji, sam dan majalisar bai halarta ba. Kungiyoyi da yawa sun taimaka wa ‘yan gudun hijirar Batsari,masallatan kungiyar Izala da Dariku da wasu shiyya na ‘yan shi’a duk sun taimaka.

Wani dandali mai suna Katsina City News da ke a whatsaap ya tara kudi ya kama gidaje da basu abinci da kai wasu marasa lafiya asibiti duk ‘yan Batsari da suka zo Katsina gudun hijira ‘yan jarida sun yi ta rubutu akan halin da yankin yake ciki, wanda ya sanya har shugaban kasa da matarsa suka je yankin a lokutta daban-daban don jajantawa mutanen yankin.

Hatta wannan jaridar ta dauki wakilan din-din guda uku don kawo abin dake faruwa, don jawo hankalin duniya wannan yasa duk wani labarin yankin daga wajensu ake fara ji.

Duk wadannan da suka faru a sama bamu taba jin dan majalisar ya fito yana godiya ba, ga wadanda suke tausaya ma halin da ake ciki. Bamu ji yayi a rediyo ko talabijin ko wata jarida ba, ko kuma ya kira masu yada sako a yanar gizo ya shaida masu su yada.

Amma abin haushi sai ga wannan dan majalisar ya raka mai ikirarin tattaki zuwa wajen mataimakin gwamnan Kano, har da yin wasu jawabai kamar na dan ma’abba. Kai Allah ya shirya naka in yana neman kaucewa.

Mu a Taskar Labarai muna ba dan majalisar nan shawara guda uku kuma da fatan Allah ya bashi ikon dauka.

1. In har gwamnatin Kano tayi masa ihsani ko kauta don rakiyar da ya wo da kuma jawaban da yayi don Allah kar ya karba yace ya gode ya kare martabar kansa, jiharsa karamar hukumar sa da kuma asalinsa na Barumaye.

2. Ya zo Katsina yayi godiya ta musamman ga wadancan bayin Allah da kungiyoyin da suka dade suna tare da jama’ar yankinsa, ya ce ajizanci ne ya jawo bai yi masu da wuri ba.

3. Yayi ma jama’ar Katsina da majalisa gamsashshen bayanin me ya sa yayi haka, ya kuma basu hakuri.

Allah ya sanya a gane.
…………………………………………………………………………
Taskar Labarai da the Links News jaridu ne guda biyu masu zaman kansu dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da www.thelinksnews.com duk wani sako a aika a katsinaoffice@yahoo.com da 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here